Daga Rukayya Abdullahi Maida
Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya mika sakon barka da sallah ga al’ummar Musulmin Kano da kasa baki daya, inda ya bukace su da su cigaba da aiki da dabi’un da suka koya a watan Ramadan.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya aikowa Kadaura24, gwamnan ya jaddada muhimmancin cigaba da dabbaka kyawawan dabi’u da tallafawa mabukata da kuma inganta zaman lafiya.

Gwamna Yusuf ya tabbatar wa al’ummar Kano kudirin gwamnatinsa na inganta rayuwarsu, ta hanyar tabbatar da ci gaban tattalin arziki, jin dadin jama’a, samar da ababen more rayuwa.
Murtala Sule Garo ya yiwa Kanawa Barka da Sallah
Da yake jawabi game da kisan gillar da aka yi wa ’yan Kano kwanan nan a Jihar Edo, Gwamnan ya nuna matukar alhininsa game da lamarin.
Ya kuma sha alwashin cewa gwamnatinsa ba za ta yi duk mai yiwuwa har sai an gano wadanda suka aikata wannan aika-aika tare da hukunta su.

Ya bukaci al’ummar Kano da su yi amfani da lokacin bukukuwan don karfafa dankon zumunci da samar da zaman lafiya.
Ya kuma yi kira al’ummar Musulmi da su yi koyi da kyawawan halaye na Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam) ta hanyar tabbatar da adalci da gaskiya da tausayi a cikin dukkan mu’amalarsu.