Yan sanda a Kano sun Gano Gawar Mace da Namiji a Mota

Date:

Yan sanda a Kano sun ce sun gano gawar mutane biyu a kurar bayan wata motar kirar Siena a kan hanyar zuwa Katsina.
 Kano Fucus ta rawaito rahotonnin sun nuna cewa binciken ya gano sunan mutumin da ya mutu a Matsayin Steven Ayika yayin da macen aka bayyana sunan ta a Matsayin Chiamaka Emmanuel dukkanin su mazauna unguwar Jaba ne dake nan Kano.
 A wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar a ranar Alhamis, ya ce: “A ranar 23/11/2021 da misalin karfe 0450 na safe, an samu rahoton cewa an ga wata mota a kan hanyar Katsina, dake karamar hukumar Fagge ta jihar Kano dauke da mutane biyu (2) a ciki, namiji daya Mace daya.
 “Bayan samun rahoton, kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, CP Sama’ila Shu’aibu Dikko, fsi, ya taso tare da umurci tawagar ‘yan sanda da su wuce wurin da lamarin ya faru.
 “Nan take tawagar ta garzaya wurin da lamarin ya faru.  An kwashe gawawwakin, inda aka garzaya da su Asibitin kwararru na Murtala Mohammed Kano, yayin wani Likitan lafiya ya tabbatar da mutuwarsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Babbar Sallah: Gwamnatin Kano ta sanar da ranar rufe makarantu a jihar

Daga Rahama Umar Kwaru   Gwamnatin Jihar Kano ta bayar da...

Ban San Taulaci ba Sai da na Zama Sarkin Kano – Sarki Sanusi II

Daga Isa Ahmad Getso Sarkin Kano na 16 Muhammadu Sanusi...

Iftila:I: Gwamnatin Kano ta Aiyana Ranar Litinin a Matsayin Ranar Hutu

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya ayyana ranar Litinin...

Kungiyar shugabannin kafafen yada labarai ta Kano ta zabi sabbin shugabanninta

Kungiyar shugabannin kafafen yada labarai ta jihar Kano ta...