Gwamnan Kano Ya Rantsar Da Sabon Kwamishinan Gidaje

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu
 Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya jagoranci rantsar da Sabon kwamishinan gidaje Ibrahim Yakubu Adamu .
 A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya aikowa Kadaura24, ya ce Kwamishinan shari’a na jihar Kano, Haruna Isah Dederi ya takabawa ba sabon kwamishinan a ranar Litinin.
InShot 20250309 102403344
Talla
 Kafin nadin nasa, Adamu shi ne Manajan Darakta na Hukumar Tsara burane ta Kano (KNUPDA).
 Da yake jawabi a wajen taron, Gwamna Yusuf ya yaba da kwarewar sabon kwamishinan da irin gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban Kano.
 Ya bayyana muhimmiyar rawar da Adamu ya taka wajen tsarawa da raya garuruwan Kwankwasiyya, Amana, da Bandirawo tsakanin 2013 zuwa 2015 a karkashin gwamnatin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
 Gwamnan ya yaba da rawar da Adamu ya taka a matsayin Kwamishinan Ayyuka da Gidaje daga 2011 zuwa 2015, inda ya taka muhimmiyar rawa wajen aiwatar da manyan ayyukan gidaje.
 Gwamna Yusuf ya kalubalanci sabon kwamishinan da ya tabbatar ya magance matsalolin gidaje a Kano, musamman wadanda suka shafi ma’aikatan gwamnati.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta sake maka Ganduje da ya’yansa a gaban Kotu

Gwamnatin jihar Kano ta kai tsohon gwamnan jihar, Dr....

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta koka da kalaman mataimakin gwamnan Kano

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta Najeriya (NANNM) reshen...

Kotu a Kano ta hukunta masu shago saboda zubar da shara a kan titi

Kotun tafi da gidanka da ke Kano ta yanke...

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...