Da dumi-dumi: An kama wani shugaban karamar hukuma a Kano

Date:

Daga Aliyu Danbala Gwarzo

 

Hukumar karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano ta kama shugaban karamar hukumar Kiru Abdullahi Mohammed bisa zarginsa da sayar da wani fili da aka tanada don yin filin kwallo a garin Kafin Maiyaki.

A binciken da hukumar ta gudanar, wani kamfani mai suna Mahasum ne ya sayi filayen da aka tanada don yin filin wasan akan kudi sama da Naira miliyan 100, inda aka saka kudaden kai tsaye a asusun shugaban karamar hukumar.

InShot 20250115 195118875
Talla

Da yake tabbatar da kamun, jami’in hulda da jama’a na hukumar, Kabir Abba Kabir, ya bayyana cewa daga 1 ga watan Nuwanba, 2024 wato lokacin da aka rantsar da shi a matsayin shugaban karamar hukumar zuwa ranar 27 ga watan Fabarairu 2025 a Asusun sa kuma tuni hukumar ta kwace kudaden.

Rahotanni sun ce Abdullahi Muhammad na bayar da hadin kai ga masu bincike a kokarin hukumar na bankado bayanan da aka yi na sayar da filin tare da hukunta wadanda suka aikata laifin.

Sabbin Matakan tsaro da ya kamata al’ummar Kano su bi a watan Ramadana -Inji Rundunar Yansanda

Hukumar ta sake jaddada aniyar ta na yaki da cin hanci da rashawa da kuma tabbatar da gaskiya a harkokin mulki, inda a halin yanzu wanda ake zargin yana hannun jami’an tsaro yayin da ake ci gaba da bincike.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi: El-Rufa’i ya fice daga jam’iyyar APC

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i ya tabbatar da...

2027: Atiku Abubakar ya bayyana matsayarsa game da kasancewarsa a PDP

  Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya musanta rahotannin...

Cikakken Bayani Kan Yan Bindigar da Yansanda Su Ka Kama a Kano

Daga Rahama Umar Kwaru   Rundunar yansanda ta kasa reshen jihar...

Gidauniyar Sheikh Dr. Muhajihid Aminudden ta rabawa magidanta 600 kayan abinchi a Kano

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Gidauniyar Dr. Muhajihid Aminudden ta rabawa...