Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, tsohon gwamnan jihar Kano, ya ce jam’iyyar NNPP za ta kayar da dukkan jam’iyyun siyasa a zabe mai inganci da adalci.
Kwankwaso ya bayyana haka ne a ranar Alhamis a taron kwamitin zartarwa na kasa (NEC) na jam’iyyar a Abuja.

Dan takarar NNPP a zaben 2023 din ya soki gwamnatin Bola Tinubu, yana mai cewa ‘yan Najeriya na fuskantar matsin rayuwa fiye da yadda aka taba gani a baya.
“Gaskiya ne da wuya a tuna da wani da ke farin ciki da gwamnatin APC a kowane mataki, musamman a matakin tarayya,” in ji shi.
“‘Yan Najeriya sun shaida wahalhalu da ba a taba gani ba a tarihin wannan kasa.
Dan Majalisar NNPP ya fice daga jam’iyyar zuwa APC
“Talauci ya yadu ko’ina. Mun ga rashin tsaro, gine-gine da ababen more rayuwa suna lalacewa, kuma ba mu ga wani kokari na gyara su ba.
“Na yi imani idan aka gudanar da sahihin zabe a wannan kasa, jam’iyyarmu za ta kayar da APC, PDP da sauran jam’iyyu.”