Hadimin Kakakin Majalisar Tarayya Abubakar Aminu ya raba fom din JAMB 250 ga Daliban Dala

Date:

Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa

 

Babban mai taimaka wa kakakin majalisar wakilai ta kasaTajudeen Abbas, Abubakar Aminu Ibrahim ya raba fom din jarabawar JAMB har guda dari biyu da hamsin ga daliban jihar Kano.

An gudanar da taron rabon fom din ne a gidan Mubayya dake Kano a ranar Litinin.

Wadanda suka ci gajiyar tallafin sun fito ne daga mazabu goma sha biyu na karamar hukumar Dala ta jihar Kano.

InShot 20250115 195118875
Talla

Da yake raba fom ga dalibin da aka zabo, Abubakar Aminu Ibrahim ya ce ya raba fom din ne saboda kishinsa ga harkokin Ilimi, inda ya ce ya yi hakan ne domin a taimaka wa marasa galihu.

Ya ce ya na shirin samar da wata gidauniyar tallafawa ilimi da za ta rika tallafa wa dalibai a karamar hukumar Dala.

Ku fito ku yiwa yan Nigeria bayanin aiyukanku – Tinubu ga Ministoci

“Na yanke shawarar raba fom din JAMB 250 ga dalibai masu karamin karfi a karamar hukumar Dala. Kuma ba wai mun gama kenan ba, za mu cigaba da bibiyarsu har sai mun ga sun sami gurbin karatu a jami’o’in da suke so.” Inji Abubakar Aminu

Ya kara da cewa, “Muna da shirin cigaba da bayar da tallafin karatu ga wasu daga cikin daliban karamar hukumar Dala a nan gaba”.

Taron ya samu halartar shugaban jam’iyyar APC n Dala, Munir Haruna, da dattawan jam’iyyar, tsofaffin shugabanni da kansiloli, da dai sauransu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Magantu Kan Batun Sheikh Abduljabbar

Hukumar Gyaran Hali ta Jihar Kano ta bayyana cewa...

Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan

Tsohon ɗan majalisar tarayya, Farouk Lawan, ya bayyana cewa...

An Dauke Shaikh Abduljabbar Daga Gidan Yari na Kurmawa Zuwa Wani Wuri – Yan uwansaba

Wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta...