Majalisar Wakilan Najeriya ta yi kira ga Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki a Fasar Zamani, Bosun Tijani, da Hukumar Sadarwa ta Ƙasa (NCC), da su dakatar da karin kudin kiran waya da na data da ake shirin yi.
Kiran ya biyo bayan amincewa da kudirin gaggawa da dan majalisa Obuku Offorji ya gabatar a zaman majalisar da aka yi ranar Talata.

Yayin gabatar da kudirin, ya bayyana cewa ministan ya bayyana a ranar Laraba, 8 ga watan Janairu, a wani taron masu ruwa da tsaki, cewa kamfanonin sadarwa za su kara farashin kiran waya da na Data a nan gaba.
A cewarsa, ana ci gaba da tuntuba, domin wasu daga cikin kamfanonin sadarwa suna kokawa kan bukatar karin kudin har zuwa kashi 100 cikin 100.
Hukumar hana cin hanci ta Kano ta kama wani Hadimin Gwamnan Kano
Sai dai ya ce karin ba zai kai kashi 100 cikin 100 ba, kuma NCC za ta amince da sabbin farashin sannan ta sanar da su a lokacin da ya dace.
Sai dai, dan majalisar ya kalubalanci hujjojin da kamfanonin sadarwa suka bayar dangane da karin kudin, wadanda suka hada da kudin saka hannun jari, inganta cibiyoyin sadarwa.