Aiyuka 5 da Gwamnan Kano ya yi alkawarin yi, bayan dakatar da rusau a Rimin Zakara

Date:

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ziyarci garin Rimin Zakara da ke karamar hukumar Ungogo domin yin ta’aziyya da jajantawa iyalan wadanda rikicin ya rutsa da su wanda ya yi sanadin asarar rayuka uku tare da jikkata wasu da dama.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya aikowa Kadaura24 a ranar Alhamis.

A ziyarar tasa, Gwamna Yusuf ya gana da iyalan wadanda suka rasu, inda ya yi musu ta’aziyya tare da bayyana cewa gwamnatin jihar za ta dauki nauyin kula da iyalan mutanen uku da suka rasu.

InShot 20250115 195118875
Talla

Ya kuma ba da umarnin a gaggauta biyan kudaden jinya ga duk wadanda suka jikkata tare da samar da kayan abinci don tallafawa iyalan wadanda abin ya shafa.

Gwamnan ya bayyana shirin gina sabon masallacin Juma’a a Rimin Zakara a matsayin sadaqatu jariya ga mutane ukun da suka rasu.

Shugaban K/H Garun Mallam zai Raba Audugar Mata 500 ga Makarantun Sakandiren Matan yankin

Bugu da kari, gwamnan ya kaddamar da shirin gudanar da wasu aiyukan cigaba a yankin na Rimin Zakara wanda ya hada da:

• Haɗa musu wutar lantarki.

• Gina rijiyoyin burtsatse masu amfani da hasken rana domin samar da ruwa mai tsafta.

• Samar da karamin asibitin sha ka tafi don inganta ayyukan kiwon lafiya.

• Samar musu da hanya don inganta sufuri a ga al’ummar Rimin Zakara.

Gwamna Yusuf ya yi kakkausar gargadi ga jami’an tsaro kan amfani da harsashi a akan al’ummar da ba su ji ba ba su gani ba, yana mai jaddada cewa ba zai lamunci hakan ba.

Hakazalika, gwamnan ya kuma baiwa mahukuntan Jami’ar Bayero umarnin su da su dakatar da duk wani mataki na yin rusau a yankin .

Rusau: Kwankwaso ya bukaci gwamnan Kano ya biya diyyar mutanen da aka kashe a Rimin Zakara

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kuma tabbatar wa al’ummar jihar kan kudirinsa na ganin an shawo kan rikicin filayen da aka kwashe sama da shekaru 40 ana yi tsakanin al’ummar Rimin Zakara da Jami’ar Bayero Kano.

Wannan batu da aka dade yana haifar da tada jijiyar wuya, kuma gwamnan ya jaddada kudirinsa na ganin an samar da maslaha mai dorewa wanda zai amfanar da dukkan bangarorin da abin ya shafa.

A yayin taron, shugaban al’ummar Rimin Zakara, Baba Habu Mikail, ya nuna matukar godiya ga gwamnan bisa yadda ya nuna tausayi, inda ya bayyana cewa al’umma ba za su taba mantawa da alherinsa ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Shugaban karamar hukuma ya biya wa al’ummarsa kudin wutar lantarki

Majalisar Karamar Hukumar Jibiya a Jihar Kastina ta biya...

Shugaban K/H Garun Mallam zai Raba Audugar Mata 500 ga Makarantun Sakandiren Matan yankin

Daga Safiyanu Dantala Jobawa Shugaban karamar hukumar garun mallam Aminu...

Inganta Noma: Sanata Barau zai tallafawa Matasa 558 daga Arewa maso yammacin Nigeria

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...

Kwamitin Majalisar Wakilai ya gabatar da shawarar kara Jihohi 31 a Nigeria

Daga Maryam Muhammad Ibrahim Kwamitin majalisar wakilan Nigeria mai kula...