Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Sakataren jam’iyyar APC na jihar Kano, Alhaji Ibrahim Zakari Sarina, ya zama kwamishinan hukumar korafe-korafen jama’a ta kasa (PCC), mai wakiltar jihar Kano.
Sarina ya maye gurbin Hon Yusuf Abdullahi Ata, wanda aka nada shi a matsayin karamin ministan gidaje da raya birane.
Ata ya kasance kwamishinan PCC mai wakiltar jihar Kano daga Yuli zuwa Oktoba 2024 kafin shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya nada shi a matsayin minista.
Gwamnatin Kano ta haramtawa yan kwangila zuwa ma’aikatar kananan hukumomi ta jihar – Kwamishina
Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Obot Akpabio, ne ya sanar da nadin Sarina a zaman na yau.
Sarina, dai yanzu haka shi ne sakataren jam’iyyar APC na jihar Kano.