Gwamnatin jihar Kano, ta ce za ta gudanar da bincike na musamman dan gano musabbabin rikicin da ya faru a unguwar Rimin zakara wanda yai sanadiyyar rasa rayukan mutane.
Kwamishinan yada labarai na jihar Kano Kwamred Ibrahim Abdullahi Waiya ne ya bayyana hakan a zantawarsa da manema labarai kan rikicin da aka samu tsakanin jami’an tsaro da mutanan dake zaune a yankin.
Waiya ya kuma ce Jami’ar Bayero ce ta nemi taimakon gwamnatin Kano dan a dawo mata da filayenta, wanda hakan yasa ta shiga tsakani kuma aka baiwa mutanan dake zaune a gurin wa’adin tashi kasancewar lokacin da aka basu ya riga ya kare.
Daga nan waiya yace bata gari ne suka shiga cikin lamarin Domin tada zaune tsaye duk kuwa da jami’an tsaron da Wadancen Mutanen suka gayyato gudun tada fitina.
Sanata Barau zai baiwa dalibai 1,000 tallafin karatu a Kano ta tsakiya da ta Kudu
Kwamishinan yada labarai da ayyukan cikin gida Kwamred Ibrahim Abdullahi Waiya yace, lallai Gwamnatin Kano zata kafa kwamitin da zai gudanar da bincike Kan Wanda suka haddasa rikicin da yayi sanadiyyar rayukan Mutane uku.
Idan za a iya tunawa Kadaura24 ta rawaito al’ummar unguwar Rimin zakara a jiya litinin sun zargi ma’aikatar Kasa ta Kano da rushe musu gidajensu da hadin kan jami’ar Bayero, lamarin da ya jawo har jami’an tsaro suka kashe mutane 4 tare da jikka wasu 16 .