Daga Nazifi Dukawa
Mazauna Unguwar Rimin Zakara da ke Karamar Hukumar Ungoggo a jihar Kano sun nuna bacin ransu bayan da suka zargi wasu jami’an tsaro tare da rakiyar motocin rushe gurare suka hallarci unguwar inda suka fara rushe gidaje da kwangayen dake yankin.
Hakan dai ya fusata al’ummar yankin har suka kone Gidan mai gari, da suka ce da shi aka hada baki aka cucesu.
Abubakar Mika’ilu mazaunin unguwar ne ta Rimin zakara ya shaidawa kadaura24 cewa suna zargin ma’aikatar Kasa da tsare-tsare ta jihar Kano da jami’ar Bayero da wata runduna ta musamman ta da kunshi jami’an tsaro daban-daban sune suka shiga unguwar tasu cikin dare domin rushe musu gidajensu.
” Anzo cikin dare za a rushe mana gidaje hakan tasa aka kashe mana yara kusan 3 tare da karbin wasu matasan guda 6 , Muna kira ga gwamnan jihar Kano da ya sa baki akan Wannan lamari domin mu ko za’a karar da mu ba mu bari a zalunce mu ba”. Inji Abubakar Mika’ilu
Guda cikin iyayen yaran da aka kashe, ya ce sun cika da mamakin yadda gwamnati da ya kamata ta kare rayukan al’umma kuma ta buge da kashe mutane.
Da dumi-dumi: Bayan dakatar da Sojaboy daga Kannywood, wata masarautar a sokoto ta tube rawaninsa
Ya bukaci gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf da ya bincika tare da hukunta duk wanda yake da hannu wajen kashe musu ya’yansu.
Ana dai fargabar jami’an tsaron sun harbi wasu mutane shida, an kuma yi jana’izar mutane biyu.
Kadaura24 ta tuntubi daraktan wayar da kan al’umma na ma’aikatar kasa ta Kano,inda ya ce suna gudanar da bincike kan lamarin, da zarar sun gama kwamishinan ma’aikatar zai sanar da mu halin da ake ciki.
Hakama, da muka tuntubi Kakakin Rundunar yan sanda ta Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce suna gudanar da bincike kan lamarin.