Jaafar Jaafar ya fallasa sunan mai kitsawa gwamnatin Kano makarkashiya a Abuja

Date:

Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa

 

Mamallakin jaridar Daily Nigerian Jafar Jafar ya ce mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata Barau Jibrin ne ya yake shirya duk wata makarkashiyar da ake yiwa gwamnatin jihar Kano a Abuja.

” Akwai bayanan sirri da muke samu wadanda suke tabbatar da cewa Sanata Barau Jibrin shi ne yake hada duk wadannan abubuwan ba kamar yadda ake zargin shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Umar Ganduje ba”.

Jaafar Jaafar ya bayyana hakan ne cikin wani shiri da suke gabatarwa a kafafen sada zumunta mai suna Fashin Baki.

InShot 20250115 195118875
Talla

Ya ce suna da kunnuwa da tawa don haka suna sami labarai ta karshin kasa, wadanda suke nuna cewa Sanata Barau shi yake amfani da damarsa a gwamnatin tarayya suke kawo wa gwamnatin jihar Kano cikas a duk wani abu da ta shirya gudanarwa.

” Wallahi Ina da kyakykyawar alaka da Sanata Barau Jibrin, amma kuma hakan ba zai hana in fadi gaskiya akan abubuwan da yake yi ba, domin wadannan abubuwan cutar da Kano suke yi”. Inji Jaafar

Gwamnatin Kano Za Ta Fara Shirin Yiwa Ali Madakin Gini Kiranye

Ya ce ya kamata Barau Jibrin ya sani cewa duk abun da yake yi yana yi ne saboda yana so ya mulki garin, ” To idan garin ya lalace ko Allah ya sa ka zama gwamnan Kano abun zai cutar da kai”.

Jaafar Jaafar dai na tsokaci ne kan abun da ya faru na kokarin hana Sarki Sanusi gudanar da taron Maulidin Shehu Ibrahim Inyass da aka yi a Kano ranar asabar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bayan shekaru 20, Kotun Ƙoli ta sanya ranar yanke hukunci kan rikicin masarautar Gwandu

Kotun Koli ta sanya ranar yanke hukunci kan daukaka...

Hukumar Shari’ah ta kaddamar da kwamatoci domin kawo sauye-sauye game da cigaban Shari’a a jihar Kano

  Hukumar Shari'ah ta jihar Kano karkashin jagorancin mukaddashin shugabanta...

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...