Hukumar tace fina-finai ta haramtawa wani jarumi da wasu mata biyu Film da waka a Kano

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Hukumar tace fina-finai da Dab’i ta Jihar Kano ta bayyana matsayarta kan korafe-korafen da al’umma suka shigar gabanta tare da wasu malamai a Jihar Kano kan Usaman Sojaboy dangane da wani sabon salon waka da yake kokarin fitowa da shi wanda ya saba da koyarwar addinin musulunci tare da al’adar malam Bahaushe.

A wata sanarwa da jami’in yada labaran Hukumar Abdullahi Sani Sulaiman ya aikowa Kadaura24, ya bayyana cewa Shugaban Hukumar Abba El-mustapha ya aminche da kwace lasisin mawakin Sojaboy da Shamsiyya Muhammad tare da Hassana Suzan ya yin da sanarwa ta bukaci masu gidajen wasanni tare duk wani wadanda suke mu’amalar aiki dasu da su yi biyayya ga wannan matakin na Hukumar domin cigaban Jahar Kano.

InShot 20250115 195118875
Talla

Abba El-mustapha ya baiwa sashin tace fina-finai na Hukumar umarnin cewa daga wannan lokacin kada a kara tace duk wani film da aka hangi fuskokinsu a ciki tare da kira ga masu shirya fina-finai musamman daraktoci da su kiyayi yin duk wata huldar aiki dasu domin gujewa fishin Hukumar.

Da dumi-dumi: NAHCON ta Kayyade Farashin kudin Aikin hajjin 2025

Kafin ta dauki irin wannan matakin Hukumar na yin iya kokarinta kan gargadar masu irin wannan halayya nasu kiyayi yin duk wani abu da zai zubar da kimarsu ko Sana’arsu inda ta Kara jaddada cewa buzata dauki duk wani abu da zai taba addini, al’ada ko tarbiyar a’lummar Jahar Kano da sauki ba. Haka kuma, bazata goyi bayan ire-iren wannan halayyar ba da sunan sana’a a Jahar Kano.

Idan ba’a manta ba a watan da ya gabata ne Hukumar ta dauki irin wannan mataki ga daya daga cikin fitattun jarumai a Masana’antar ta kannywood wato Samha M Inuwa da nufin tsaftace Masana’antar tare da tabbatar da kowa nabin dokokin Hukumar sau da kafa.

A kwanakin baya dai an gano Sojaboy yana rungumar wasu mata a wasu sabbin wakoki da ya fitar, sai dai hakan ya jawo cece-ku-ce a tsakanin al’umma har ma da su yan masana’antar Kannywood.

Sai dai a wata hira da akai da shi, Sojaboy ya ce yayi hakan ne domin fito da wani sabon salo da zai sa a rika kallon wakoki ko fina-finan Kannywood a ko ina a duniya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi: Kotu ta aike da Matashin dake shigar mata a Tiktok da film gidan gyari

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Shugaban Hukumar tace fina-finai da Dab'i...

Rabon Jakai: Faizu Alfindiki ya aikawa Sanusi Bature budaddiyar wasika

Zuwa ga: DG. Sunusi Bature Dawakin Tofa Daraktan Yada Labarai, Gwamnatin...

Dama ba mu yi shirin yin hawan babbar Sallah ba – Sarki Aminu Ado Bayero ya fadi dalili

Daga Isa Ahmad Getso   Sarkin Kano na 15 Aminu Ado...

Abdullahi Muhammad ya zama sabon shugaban kungiyar NUJ Pyramid Radio

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Mai rikon mukamin shugaban kungiyar yan...