Abdullahi Muhammad ya zama sabon shugaban kungiyar NUJ Pyramid Radio

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Mai rikon mukamin shugaban kungiyar yan Jarida ta Kasa reshen jihar Kano Mustapha Gambo Muhammad ya rantsar da Sabon shugaban kungiyar reshen gidan Radio Nigeria Pyramid Fm Kano.

Da yake jawabi Mustapha Gambo ya bukaci Sabon shugaban da ya Maida hankali wajen hada kan ya’yan kungiyar domin samar da cigaba mai ma’ana .

IMG 20250415 WA0003
Talla

“Hadin Kai shi ne kashin bayan cigaban Kowacce al’umma, don haka ina kira a gareka da kai yi iya bakin kokarinka don samar da hadin Kai wanda shi ne zai Kai Wannan kungiya ga sabon cigaba”. Inji Mustapha Gambo Muhd.

Mukaddashin shugaban na NUJ ya kuma yi kira ga ya’yan kungiyar da sauran Shugabannin kungiyar da su baiwa Sabon shugaban hadin kai da goyon baya domin ya Sami nasarar ciyar da kungiyar gaba.

Yansanda sun Haramta Hawan Sallah a Kano

Da yake nasa jawabin sabon shugaban kungiyar yan jarida reshen gidan Radio Nigeria Pyramid Abdullahi Muhammad ya yi alkawarin yin aiki bisa Gaskiya da adalci ba tare da nuna banbanci ba .

” Babu shakka wannan muhimmiyar rana ce a wajena da ita wannan kungiya, kuma Ina ba ku tabbacin na zo da Tsare-tsare da za su ciyar da kungiyar nan ta mu gaba”. Inji Abdullahi Muhammad

Ya ce ya na kira ga daukacin ya’yan kungiyar da su ba shi hadin Kai da goyon baya domin aiwatar da tsare-tsaren da ya zo da su don inganta cigaban kungiyar da Samar da walwala ga ya’yan kungiyar.

InShot 20250309 102403344

Abdullahi Muhammad dai ya maye gurbin Aminu Abba Kwaru ne wanda ya Sami sauyin wurin aiki daga Pyramid Fm zuwa Ma’aikatar Kula da ingantuwar aiyuka ta Kasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bayan tura Kashim ya taho da gawar Buhari, Tinubu ya ba da umarnin sassauta Tutar Nigeria

Shugaban kasa Bola Tinubu ya bada umarnin ayi kasa...

Yanzu:yanzu: Tsohon shugaban Nigeria Buhari ya rasu

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un!!! Allah yayi wa tsohon shugaban...

Tinubu ka fadawa yan Nigeria Inda ka tsaya har kwana 5 bayan taron BRICS – ADC

    Jam'iyyar African Democratic Congress wato ADC ta soki Shugaban...

Da dumi-dumi: Yadda akai Jami’an tsaro suka kama ni -Danbello

Rahotannin sun tabbatar da cewa jami'an tsaro a Nigeria...