Da dumi-dumi: NAHCON ta Kayyade Farashin kudin Aikin hajjin 2025

Date:

Daga Sidiya Abubakar

Hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON a karkashin jagorancin shugabanta Farfesa Abdullahi Saleh Usman ta sanar da kudin tafiya aikin hajjin bana, an dai sanar da kudin ne bayan amincewar ofishin mataimakin shugaban kasar tarayyar Najeriya.

Hakika Shugaban Hukumar NAHCON da tawagarsa tare da hadin gwiwar wakilin fadar shugaban kasa, Malam Ameen Amshi, wanda shi ne mataimaki na musamman ga shugaban kasa, ayyuka na musamman sun yi iyakacin kokarinsu wajen ganin an fitar da kudin aikin Hajji daidai da yadda aka biya a baya.

A sanarwar da mataimakiyar daraktar yada labarai ta hukumar, Fatima Sanda Usara ta sanyawa hannu, tace an cimma wannan matsayar ne bayan tattaunawa mai zurfi don tabbatar da an saukakawa maniyatan Nigeria.

InShot 20250115 195118875
Talla

An dai kayyade kudin aikin hajjin ne la’akari da bisa da kuma shiyyoyin kasar kamar haka:

shiyyar Borno da Adamawa, ana sa ran maniyyata za su biya Naira miliyan 8,327,125.59 ( miliyan takwas da dubu dari uku da ashirin da bakwai, da dari da ashirin da biyar da Naira hamsin da tara kobo).

Badakalar wutar lantarki: Ba mu tilastawa Buhari zuwa ba da shaida a Kotun Paris ba – Fadar shugaban ƙasa

Maniyyatan da Suka fito daga jihohin Kudancin Nigeria kuma za su biya Naira 8, 784, 085.59 (miliyan takwas, da dubu dari bakwai da tamanin da hudu, Naira tamanin da biyar Naira kobo hamsin da tara).

Maniyyatan da suka fito daga shiyyar Arewa za su biya Naira miliyan 8, 457,685.59 ( miliyan takwas da dubu dari hudu da hamsin da bakwai, da dari shida da tamanin da biyar Naira hamsin da tara kobo).

Farfesa Saleh ya yabawa daukacin tawagar inda ya bayyana cewa an fitar da kudin aikin Hajjin da hadin gwiwa da duk masu ruwa da tsaki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bayan tura Kashim ya taho da gawar Buhari, Tinubu ya ba da umarnin sassauta Tutar Nigeria

Shugaban kasa Bola Tinubu ya bada umarnin ayi kasa...

Yanzu:yanzu: Tsohon shugaban Nigeria Buhari ya rasu

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un!!! Allah yayi wa tsohon shugaban...

Tinubu ka fadawa yan Nigeria Inda ka tsaya har kwana 5 bayan taron BRICS – ADC

    Jam'iyyar African Democratic Congress wato ADC ta soki Shugaban...

Da dumi-dumi: Yadda akai Jami’an tsaro suka kama ni -Danbello

Rahotannin sun tabbatar da cewa jami'an tsaro a Nigeria...