Daga Sani Idris Maiwaya
Gwamnatin jihar Kano ta Amince da kashe Sama da Naira Miliyan 87 dan aiwatar da Aikin Shimfida Interlock a sakatariyar Karamar Hukumar Dala
Shugaban Karamar Hukumar Alhaji Surajo Ibrahim Imam shi ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da Jami’ar Hulda da Jama’a ta Karamar Hukumar Dala Hassana Aminu ta aikowa Kadaura24.

Shugaban Karamar Hukumar Dala Surajo Imam yan a mai cewar tun Alif 1989 da kafuwar Karamar Hukumar ba ta samu wani sauyi ba sai a wannan lokacin.
Yansanda sun Haramta Hawan Sallah a Kano
Ya kara da cewar hakan ya na daga cikin manufofin gwamnatin Kano na kawo sauyi da Cigaba Mai ma’ana a matakai daban daban
Surajo Imam yace izuwa yanzu tuni an biya Sama da Miliyan 47 na kudin Aikin, Yana Mai cewar baya Ga wannan kuma akwai Wani Shirin na fentin Karamar Hukumar Dalan da sauya kofofi, Hadi da Gina sabuwar majalisar Kansiloli bisa irin hadin kai da suke Bashi dan Ciyar da Karamar Hukumar Gaba.
A Jawabin Sa Shugaban sashin Ayyuka na Karamar Hukumar Dala Alhaji Shafi’u Musa Zakarai ya bayyana da Kaddamar wannan mahimmin Aiki da nufin zamunantar da Karamar Hukumar Dala
Shi ma a nasa bangaren Malam Shafi’u Gwarzo bukaci ma’aikatan karamar hukumar da su kula da kayayyakin aikin da aka samar domin amfanin su yadda ya kamata, dan ciyar da yankin Gaba.