Dama ba mu yi shirin yin hawan babbar Sallah ba – Sarki Aminu Ado Bayero ya fadi dalili

Date:

Daga Isa Ahmad Getso

 

Sarkin Kano na 15 Aminu Ado Bayero, ya sanar da dakatar da duk wani shirin hawa ko haye-haye da aka saba gudanarwa yayin bukukuwan babbar Sallah na bana a Kano .

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun Sakataren masarautar, Awaisu Abbas Sanusi, wadda aka fitar a ranar Talata .

IMG 20250415 WA0003
Talla

Wasikar da tura ta ga hakiman Masarautar Kano ta ce, an yanke wannan shawara ne bayan tattaunawa da hukumomin tsaro da kuma yan majalisar Sarki.

Sanarwar ta ce, “Duk da cewa tun farko an janye shirin hawa domin ƙara tabbatar da zaman lafiya, yanzu kuma an dakatar da haye-haye baki ɗaya saboda wasu dalilai da suka haɗa da haɗurran da suka faru a baya ga wasu matasa ‘yan jihar Kano da ke dawowa daga Abeokuta, da kuma sanarwar da rundunar ‘yan sandan jihar ta fitar wacce ta haramta gudanar da kowanne irin hawan doki ko gangami a lokacin Sallah.”

InShot 20250309 102403344

Majalisar ta kuma jaddada cewa Fadar Kano gida ne da ke tsayawa kan doka da oda, ta na kuma haskaka wa al’umma turbar da za ta ba su damar rayuwa cikin mutunci da zaman lafiya.

“Zaman lafiya yafi komai, don haka ya zama dole mu kasance masu haƙuri da kaucewa duk wani abu da zai iya haddasa rikici ko tayar da hankali,” in ji sanarwar.

Za a kashe Naira Miliyan 87 wajen Sanya Interlock a sakatariyar K/H Dala – Surajo Imam

Sanarwar ta kuma bukaci iyaye su kara kula da ƴaƴansu, tare da hana su shiga cikin duk wani abu da zai kai ga tashin hankali ko barazana ga zaman lafiya.

Daga karshe, an yi addu’ar Allah ya dawo da dukkan alhazan Kano lafiya daga ƙasa mai tsarki tare da yi wa al’ummar jihar fatan gudanar da bikin Sallah cikin kwanciyar hankali da albarka

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Zargin Almundahana: ICPC zata gurfanar da shugaban hukumar zabe ta Kano da wasu mutum biyu

    Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta (ICPC)...

Dalilin da ya hana ni zuwa Kano tarbar Tinubu – Ganduje

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa,...

Shugaban RATTAWU na Kano ya taya sabbin shugabannin kungiyar na kasa murna

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Shugaban kungiyar ma’aikatan rediyo, Talabijin da...

Dalilina na ziyartar gwamnan Kano Abba – Inuwa Waya

Daga Rahama Umar Kwaru Tsohon Wanda ya nemi Zama Dan...