Gwamnatin tarayya ta bayyana lokacin da za a kammala titin Kano – Abuja

Date:

 

Gwamnatin Tarayya ta ce nan da watanni 14 za a kammala aikin gyaran titin Abuja zuwa Kaduna zuwa Kano.

Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris, ne ya sanar da haka a yayin ƙaddamar da aikin rukunin farko na aikin daga Abuja zuwa Kaduna a ranar Alhamis.

Rukunin farko na aikin ya tashi nema daga Abuja zuwa Kaduna, kashi na biyu kuma Kaduna zuwa Zariya, sai kashi na uku daga Zariya zuwa Kano.

InShot 20250115 195118875
Talla

Ministan ya ce Ministan Ayyuka David Umahi ya bayyana cewa an kawo ƙarshen siyasar aikin gyaran titin, kuma Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ba zai lamunci jan ƙafar aikin ba.

Ya ce, “shi ya sa aka karɓe aikin daga kamfanin Julius Berger saboda suna so sai shekara uku za su kammala, amma muka ce a wata 14 muke so.

Dalilin da yasa Jaruma Maryam Labarina ta ke shan yabo

“Wannan ya sa aka raba aikin aka ba wa kamfanoni uku domin sauƙaƙa aikin. Saboda ’yan Najeriya sun ƙosa kammala aikin.

Shugaban Ƙasa ya ba da umarni kuma Majalisar Dokoki ta Ƙasa ta ba da haɗin kan da ake buƙata don haka na za a samu matsala ba.

“Nan da wata 14 za mu fara aiki da sabon titi daga Abuja zuwa Kano,” in ji Ministan.

A nasa ɓangaren, Umahi ya bayyana cewa za a tsawaita aikin da kilomita biyar zuwa Filin Jirgin Sama na Malam Aminu Kano, da kuma wani kilomita biyar ta ɓangaren Abuja zuwa Lakwaja.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...