Al’umma musamman a kafafen sada zumunta na cigaba da yabawa jarumar shirin Labarina wato Fatima Hussain (Maryam Labarina) saboda irin shigar mutunci da jarumar ta yi yayin wani bikin ba da lambobin yabo ga wasu Jaruman Kannywood a Kano.
A ranar larabar makon nan ne aka ba da lambobin yabo ga wasu hazukan Jaruman Kannywood wanda aka yiwa tarin taken PANDORA AWORD, Wanda kuma jarumai da yawa Maza da mata suka sami lambobin yabon.

Jaruma Maryam Labarina ya bayyana a wurin taron ne da shigar da ta saba da ta sauran jarumai yan uwanta Mata, inda ya yi shigar doguwar rika ne mai yalwa wadda ta boye surar jikinta.
Babu shakka shigar jarumar ta burge mutane da dama wanda hakan yasa suka rika yaba mata a kafafen sada zumunta, ga misali wasu daga ciki:
Abdulmumin Isa Kaita ” Gaskiya kin burgeni da baki yi shigar iskanci ba, Allah ya kara daukaka Maryam Labarina”.
Dole mu sulhunta Kwankwaso da Ganduje – Abdulmumin Kofa
” Wow Wannan shigar taki ta mutunci ce gashi ta rufe duk jikinki gaskiya kin kyauta. Congratulations Fatima Hussain Maryam Labarina”. A cewar Hafiza Ahmad
Abubakar Adamu cewa yayi ” Ke dai Allah ya saka miki da alkhairi, kin yi shigar mutunci tabbas mutuncinki ya karu a wajena, Ina taya ki murna”.
Wadannan kadan kenan daga irin yabon da jaruma Fatima Hussain Maryam Labarina take sha sakamakon shigar mutunci a lokacin da zata karbi lambar yabo ta PANDORA AWORD.
Da take jawabi a wajen taron ta ce ta sadukar da lambar yabon da ta samu ga masoyanya, inda ta ce ba don gudunmawar da suke bata ba da ba ta sami lambar yabon ba.
” Ina godiya ga wadanda suka shirya wannan taron, sannan Ina sanar da duniya cewa duk da sai da nayi aiki tukuru sannan suka sanni, amma dai na sadaukar da wannan Aword din ga dukkanin masoyana ba don suna kallona ba da ban kawo wannan matsayin ba”.
Jarumai da dama ne dai suka sami lambobin yabon daga cikinsu har da Abale, Aminu saira, Zahra daimon Mome Gombe da dai sauransu.