Gwamna Abba Kabir Yusuf ya raba kayan makaranta ga dalibai 789,000 dake makarantun gwamnati 7,092 a fadin kananan hukumomin jihar 44, a wani muhimmin mataki na kawo sauyi a fannin ilimi na jihar .
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Kano Sunusi Bature Dawakin Tofa ya aikowa Kadaura24.
Sanarwar ta ce, an raba tallafin ne da nufin samar da ingantaccen yanayin koyo ga dukkan yaran jihar.
Da yake jawabi a wurin rabon tallafin, Gwamna Yusuf ya jaddada kudirinsa na sake fasalin tsarin ilimin Kano.
“Wannan shi ne mafari, bayan samar da wadannan kayan makatantar, za mu ci gaba da wadata makarantunmu da karin kayan aiki don inganta yanayin koyo da king yarwa a makarantunmu,” in ji shi.
Dalilan da Suka a Fuskar Doka Har Yanzu Aminu Ado Bayero ne Sarkin Kano – M A Lawan
Baya ga kayan makatanta( Uniform), gwamnatin jihar ta raba tebura 53,000 ga makarantu domin magance matsalolin da ake fuskanta na rashi abun zama a makarantun.
Wannan mataki ya nuna yadda Gwamna Yusuf da gwamnatinsa suka damu da harkar ilimi a jihar Kano.