Dalilan da Suka a Fuskar Doka Har Yanzu Aminu Ado Bayero ne Sarkin Kano – M A Lawan

Date:

Daga Sidiya Abubakar

 

Tsohon kwamishinan shari’a na jihar Kano Barr. M A Lawan ya yi karin haske game da hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke ranar Juma’a Kan danbarwar Masarautar Kano.

Lawan, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce gwamnatin jihar Kano ta yi wa hukuncin gurguwar fahimta, inda ya jaddada cewa hukuncin kotun daukaka kara biyu ne, daya ya soke hukuncin da babbar kotun tarayya ta yanke, dayan kuma ya soke hukuncin babbar kotun jihar Kano ta yi .

“Da na ji abubuwan da gwamnatin Kano ta fadawa yan jaridu akan hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke game da rikicin masarautar Kano, hakan tasa na ga ya dace na mayar da martani kamar haka;

Talla

“Sabanin fahimtar gwamnatin jihar Kano, kotun daukaka kara ba ta tabbatar da dokar majalisar masarautu ta 2024 da ake takaddama a kai ba, haka zalika kotun daukaka kara ba ta tabbatar da sa hannu da nade-naden da gwamnan Kano ya yi game da dokar masarautun jihar Kano ba.

Ya ce Wadanda suka cire son zuciya sun fahimci cewa hukuncin kotun daukaka kara biyu ne. Daya ya soke hukuncin da babbar kotun tarayya ta yanke kan hurumin kotun na sauraren karar, daya kuma ya soke dukkan hukuncin da babbar kotun jihar Kano ta yanke.

Gwamnatin Kano ta wajabta wa motocin haya ajiye kwandon zuba shara

“Hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke game da hukuncin da babbar kotun tarayya ta yanke ya nuna cewa babbar kotun tarayya ba ta da hurumin sauraren shari’ar masarauta. Hukuncin bai goyi bayan duk wani matakin da gwamnatin jihar Kano ta dauka ba.

“Ya kamata a lura da cewa hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke na soke hukuncin da babbar kotun tarayya ta yanke a kara mai lamba 1. FHC/KN/CS/182/2024 na mai shari’a Liman akan rashin hurumin kotun  ba shi da alaka da hukuncin da mai shari’a Amobeda na babbar kotun tarayya ya yanke a kara mai lamba 1. FHC/KN/CS/190/2024. Karar da Mai shari’a Liman ya yanke ita ce wacce Alhaji Aminu Babba Dan Agundi ya shigar

“A daya bangaren kuma, lokacin da gwamnan jihar Kano ya umarci ‘yan sanda da su kamo mai martaba Aminu Ado Bayero, sai mai martaba ya shigar da kara a gaban kotu domin a kwato masa hakkinsa na tsorata shi da akai, shi ne Mai shari’a Amobeda ya yanke hukuncin da ya dace a shari’ar, inda ya bukaci gwamnatin Kano ta baiwa mai Martaba Sarki Aminu Ado Bayero Naira miliyan 10,000,000.00 . Wannan hukunci dai yana nan daram kamar yadda kotun daukaka kara ba ta yi wani bayani ba kan hukuncin da mai shari’a Amobeda ya yanke. Har yanzu ana ci gaba da sauraron karar. A cewar M A Lawan

 

A daya bangaren kuma, hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke ya tabbata da mai martaba Aminu Ado Bayero da sauran masarautu 4 na Bichi, Gaya, Rano da Karaye a matsayin sarakuna. Domin tun da farko babbar kotun jihar Kano ta yanke hukuncin kar su kara kiran kansu a matsayin sarakuna bisa dogaro ga sabuwar dokar masarautar ta 2024 tare da bayar da umarnin tsige mai martaba Aminu Ado Bayero.

“Abin da ya kamata a lura da shi, shi ne gwamnatin jihar Kano ce ta shigar da kara a gaban babbar kotun jihar da ke neman kotun ta umarci mai martaba Sarkin Kano Aminu Ado Bayero, Kar ya sake bayyna kansa a matsayin Sarkin Kano a karshe kuma babbar kotun ta amince da rokon gwamnatin tare da tabbatar da abun da gwamnatin ta yi na dawo Alhaji. Muhammad Sunusi II. Yanzu haka dai kotun daukaka kara ta yi watsi da hukuncin da babbar kotun ta yanke tare da bayar da umarnin sake sauraren karar a gaban wani alkalin babban kotun jihar Kano.

M A Lawan ya ce bisa la’akari da wadancan hukunce-hukunce da kotun daukaka kara ta yanke, ya kara tabbatar da cewa Alhaji Aminu Ado Bayero shi ne halastaccin Sarkin Kano ba Alhaji Muhammad Sunusi II.

“Ina mika godiyata ga bangaren shari’a bisa yadda suke kiyaye ka’idoji da yi Adalci a wannan shari’ar. Ina shawartar gwamnatin jihar Kano da ta daina yaudarar kanta da al’umma cewa hukuncin da kotun daukaka kara ita ya dadadawa. Sannan Ina kira ga al’ummar jihar Kano da su ci gaba da baiwa dukkanin masarautun Kano 5 da Bichi da Gaya da Rano da kuma Karaye goyon bayan da suka dace”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dr. Kabiru Getso Ya Mika Ta’aziyya Ga Iyalan Buhari

Daga Rahama Umar Gwaru   Tsohon kwamishinan ma'aikatun lafiya da muhalli...

Gwamnatin tarayya ta ayyana Ranar hutu saboda rasuwar Buhari

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ayyana Talata, 15 ga watan...

Injiniya Iliyasu Usman Salihu ya zama Jakadan zaman Lafiya na Africa

    Injiniya Ilyasu Uasman Salihu, Manajan Darakta na Sadex Engineering...

Halin da ake ciki game da shirye-shiryen jana’izar Buhari

Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda, ya bayayna cewa sai...