Kamfanin rarraba hasken wutar lantarki reshen babban birnin tarayya Abuja, ya ce wasu sassan birnin za su fuskanci katsewar lantarki na aƙalla makonni biyu.
Kamfanin na AEDC ya sanar da haka ne rana Juma’a a shafinta na X, inda ta ce za a fara fuskantar rashin wutar daga ranar Litinin da ke tafe.
Ta ce hakan zai faru ne sakamakon gyara da kuma komawa zuwa babban layin ba da wuta na megawatt 33 da kuma layin da ke bayar da wuta na megawatt 132 da ke Kukwaba.
A cewar kamfanin, za a yi aikin komawa babban layin ne daga ranar Litinin 6 ga watan Janairu zuwa 31 ga watan.
“Anguwannin da ɗaukewar lantarkin zai shafa sun haɗa da Lugbe da Airport Road da Kapwa da NNPC da Games Village da kuma National Stadium,” in ji sanarwar da kamfanin ya fitar.
Hukumar Tace Fina-fina ta Kano ta Dakatar da Babbar Jaruma a Kannywood
Ya ce sauran sun haɗa da Gudu da Gbazango da sassan Kubwa da Bwari da Jahi da sassan Jabi da Karu da Nyanya da Mararaba da kuma Keffi.
Ya ce sauran sun haɗa da Gudu da Gbazango da sassan Kubwa da Bwari da Jahi da sassan Jabi da Karu da Nyanya da Mararaba da kuma Keffi