Daga Isa Ahmad Getso
Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya amince da nada Hon. Musa Iliyasu Kwankwaso a matsayin Daraktan Kuɗi na hukumar raya kogunan Hadejia -Jama’ar mai kuda da kano.
Kafin wannan nadin Musa Iliyasu Kwankwaso mamba ne a Majalisar Ƙoli ta wata makarantar gaba da sakandire dake jihar Kogi.

A baya da Musa Iliyasu Kwankwaso ya rika mukamin kwamishina har sau uku a gwamnatin jihar Kano, Inda ya yi aiki da Malam Ibrahim Shekarau da Abdullahi Umar Ganduje.
Idan za a Iya tunawa Kadaura24 ta rawaito shugaban ƙasar ya nada Engr. Rabi’u Sulaiman Bichi a matsayin Manajan daraktan Kogunan Hadejia – Jama’are mai kula da Kano.