Gwamnan jihar kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya zargi yan jam’iyyar adawa da kokarin kawo rashin zaman lafiya jihar saboda manufarsu ta siyasa.
” Ganin da suka yi an sami zaman lafiya cigaba na shigowa jihar kano shi yasa marasa kishin jihar kano yan adawa suke kokarin sai sun dukufar da jihar ta koma baya, to Muna fada musu ba za mu lamunci hakan ba”.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin taron majalisar zartarwa ta jihar da ya jagoranta a wannan rana ta laraba.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Sanusi Bature Dawakin Tofa ya aikowa kadaura24, ya ce gwamnan ya ce binciken jami’an tsaro ya tabbatar da cewa yan jam’iyyar adawa ne suka haifar da fadan daban da akwai kwananan a Kano.
Ya ce gwamnatin jihar kano ba zata lamunci wannan Mummunar dabi’ar ba, zata dauki tsauraran matakai domin ganin an yi maganin duk wanda ya sake haifar da rashin zaman lafiya a jihar Kano.
” Za mu cigaba da aiki da hukumomin tsaro dake aiki a jihar kano domin tabbatar da zaman lafiyar jihar, da kuma magance duk wani yunkuri na haifar da rashin zaman lafiya a wannan jihar ta mu ta Kano”. Inji Gwamna Abba Kabir
Idan za a iya tunawa kadaura24 ta rawaito a yan kwanakin nan an sha fama da fadan daba a wasu unguwannin birnin kano, wanda hakan ya haifar da asarar rayuka da dukiyoyin al’umma.