Daga Kamal Yakubu Ali
Shugaban majalisar shura na Darikar Tijjaniyya ta kasa Khalifa sheikh sani shehu maihula ya yabawa gwamnan jihar kano Alhaji Abba Kabir Yusuf bisa nadin da ya yiwa Sakataren Majalisar Shura ta Darikar Tijjaniyya na kasa Barrister Imam Sheikh Habibu Muhammad Dan Almajiri fagge a Matsayin sabon shugaban hukumar Zakka da Hubusi ta jihar kano .
” A madadin daukacin mabiya darikar Tijjaniyya Muna godiya gwamnan Kano bisa yadda ya zabo daya daga cikinmu ya bashi wannan muhimmin aiki na tarawa da rana zakka ga masu Karamin karfi dake cikin al’umma”.

Shugaban Majalisar Shurar ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya aikowa Jaridar Kadaura24 a ranar juma’a.
Sheikh Khalifa sani mai hula yace hakika an ajiye kwarya a gurbinta, duba da irin gagarumar gudunmawar da Barr. Dan almajiri ya ke baiwa al’umma ,inda ya bayyana barrister Dan àlmajiri a matsayin jajirtacce wajan gudanar da ayukansa ba tare da nuna gazawa ba.
Da dumi-dumi: Gwamnan Kano ya sake baiwa sagagi mukami tare da sabbin nade-nade
Khalifa sani shehu maihula ya bukaci gwamnatin jihar kano data bashi goyan bayan da ya dace domin ganin ya dawo da martaba hukumar, kasancewarsa gogagge wanda ya saba gudanar da muamaloli da mutane daban-daban a fannoni na rayuwar .
A karshe ya yi addu’ar ga barrister Dan almajir ya kuma yi masa fatan sauke nauyin da aka dora masa da kuma neman taimakon ubangiji a yayin gudanarda ayyukansa .
.