Me ke janyo cin-zuma, me ye matsalarsa kuma me ye maganisa? – Masana sun yi bayani

Date:

 

Cin-zuma, wato “dental flourosis” lalurar haƙora ce da ke sauya launin haƙora zuwa ruwan ƙasa-ƙasa.

Lalurar tana samun yara ne, musamman ƴan shekara takwas ko ƙasa, kafin haƙoran girma su fito masu.

Dalilin cin-zuma na da alaƙa da shan ruwa mai ɗauke da sinadarin “flouride” fiye da ƙima ko kuma wasu hanyoyi da yaran za su iya ci ko shan sinadarin “flouride” fiye da ƙima.

Sinadarin “flouride” ana amfani da shi wajen tsabtace ruwan sha, sai dai kasancewarsa fiye da ƙima cikin ruwa na iya jefa ƴara cikin haɗarin samun cin-zuma.

Talla

Cin-zuma lalurar haƙora ce da ke munana haƙoran kawai, amma ba ta da illa ga lafiyar haƙoran!

Manya waɗanda suka gama haƙoran girma kuma ba su sha sinadarin “flouride” fiye da ƙima ba lokacin suna yara, to ba su da haɗarin samun cin-zuma.

Da dumi-dumi: Gwamnan Kano ya sake baiwa sagagi mukami tare da sabbin nade-nade

Lalurar cin-zuma ba ta raunana haƙora, a maimakon haka ma sai dai ta ƙarfafa haƙoran. Saboda masu cin-zuma suna da ƙarin kariyar samun ramin haƙora. Dalili kuwa shi ne sinadarin “flouride” na da muhimmanci ga lafiyar haƙora. Kawai dai ba a so ya yi yawa ne fiye da ƙima lokacin girman ƴara domin kiyaye cin-zuma.

Idan kana da cin-zuma kuma kana da damuwa kan launin haƙoran ko kuma kana da ƙorafin ciwon hakori, tuntuɓi likitan haƙori.

Daga Physiotherapy Hausa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Shugabannin Hukumomi a Kano Sun Yaba Da Ayyukan Abba, Sun Nemi Ya Nemi Wa’adi Na Biyu

Kungiyar shugabannin hukumomi da ma'aikatun gwamnatin jihar Kano ta...

Idan mu ka rungumi Addu’o’i ba abun da Amurka za ta iya yiwa Nigeria – SKY

Shahararren ɗan kasuwa a Kano, Alhaji Kabiru Sani Kwangila...

Shugaban APC na Kano Abdullahi Abbas ya Magantu Kan Zargin raba Ramat da Kujerarsa

Shugaban jam’iyyar APC na Jihar Kano, Alhaji Abdullahi Abbas,...

Iftila’i: An tsinci gawar wata dattijuwa mai shekaru 96 cikin rami masai a Kano

A ranar Alhamis al’ummar ƙauyen Sarai da ke ƙaramar...