Gwamnatin Kano ta Sauya wa Jami’ar Yusuf Maitama Sule Suna

Date:

 

A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf karo na 21 wanda aka gudanar jiya Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) majalisar ta amince da maido da suna Jami’ar Yusuf Maitama Sule zuwa sunanta na asali Northwest.

Zaman majalisar zartarwa ta Kano karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf, ta tabbatar da hakan bisa dogaro da dalilin da yasa aka kafa Jami’ar a shekara 2012 domin haɗin kan jihuhin arewa maso yamma don haɓaka ilimi a lardin, don haka aka sake maido da suna jami’ar na (North-West University).

Talla

Haka kuma majalisar zartarwa ta musanya sunan College of Education and Advanced Studies, Ghari da suna Dr. Yusuf Maitama Sule, marigayi Dan masani Kano, domin girmamawa ga Dattijon kuma uban ƙasa wanda ya hidimtawa al’ummar kasar nana baki ɗaya.

 

Da yake karin haske game da waɗanan sabbin canje-canje, Kwamishina Ma’aikatar Ilimi Mai Zurfi, Dakta Yusuf Kofarmata ya ce sabuwar makarantar (College of Education and Advanced Studies, Ghari), an canja mata suna zuwa ( College of Yusuf Maitama Sule), majalisar zartarwa ta Kano ta amince da dokar gudanarwar makarantar a zamanta na yau, inda za tai kafada-da- kafada da takorata wato kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.

Mahalarta Taron “KILAF 24” Sun Yaba da Yadda Kano ta Adana Kayan Tarihinta

Haka zalika makarantar koyan aikin Gona ta Audu Bako Dambatta da kuma makarantar Malam Aminu Kano mai laƙabin Legal, dukkaninsu za su cigaba da amsa sunayensu kamar yadda suke domin girmamawa da kuma tunawa da gudunmawar da manyan mutanen da aka sanya sunayen su suka bada.

Dakta Kofarmata ya ce tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoki zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu.

Ya godewa gwamnatin jihar musamman Gwamna Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf bisa na mijin ƙoƙarin sa na haɓaka ilimi a jihar Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Iftila’i: Almajirai 17 sun kone kurmus 15, sun jikkata sanadiyya wata gobara

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Wata gobara da ta tashi ta...

Mun gano yadda yan Bauchi ke mamaye dazukan Kano – Gwamnatin Kano

Daga Nazifi Dukawa     Gwamnatin jihar Kano ta ce ta gano...

Gwamnatin Kano Ta Kammala Aikin Gina Mayanka ta Naira Biliyan 1.5

Daga Zakaria Adam Jigirya     Gwamnatin jihar Kano ta karkashin Shirin...

An dakatar da Shugaba da Sakataren kungiyar APC X Eagle forum

Kwamitin zartarwa na kungiyar APC X Eagle forum ya...