Wata Kungiya ta gargaɗi tsohon Minista Gwarzo ya daina sukar Tinubu saboda cire shi

Date:

Daga Rahama Umar Kwaru

 

Kungiyar Renewed Hope Ambassadors Forum (RHAF) ta gargadi tsohon karamin ministan gidaje da raya birane, Abdullahi T. Gwarzo da ya daina sukar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu Saboda an cire shi daga mukamin Minista.

An sallami Gwarzo da wasu mutane hudu ne a watan da ya gabata saboda gazawarsa wajen sauke nauyin da aka dora musu a ma’aikatun da aka tura su.

A wata hira da Sashen Hausa na BBC a ranar Asabar, Gwarzo ya yi ikirarin cewa cire shi daga Minista yana da alaka siyasa. Ya koka bisa nadin da shugaba Tinubu ya yi wa Hon. Yusuf Abdullahi Atta a matsayin magajinsa. Ya kuma ce kamata yayi shugaban kasa ya nada Nasiru Yusuf Gawuna, dan takarar gwamna na jam’iyyar APC a jihar Kano a 2023, a maimakon Atta.

Talla

Gwarzo ya kuma yi karin bayani kan tattaunawar sirri da ya yi da shugaban kasar dangane da tsige shi.

A martanin da kungiyar Renewed Hope Ambassadors Forum ta mayar, ta bayyana kalaman Gwarzo a matsayin cin fuska ga shugaba Tinubu da fadar shugaban kasa, inda ta bayyana cewa kalaman nasa sun nuna bai dace da mukamin minista ba.

Wata Jami’a a London ta Baiwa Baffa Babba Danagundi Digirin Girmamawa

Ko’odinetan kungiyar na jihar Kano, Kwamared Danjuma Usman Gwale, a wata sanarwa da ya aikowa kadaura24, ya nuna rashin jin dadinsa bisa yadda Gwarzo ya yi wa sashe na 171 na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya na shekarar 1999 karan tsaye, wanda ya bai wa shugaban kasa ikon nadawa ko cire kowanne minista.

“Mun kalli hirar da BBC ta yi da korarren ministan gidaje da raya birane, Abdullahi T. Gwarzo, a matsayin cin fuska da suka ga shugaba Tinubu, wanda ke da ikon nada ministoci da korar ministoci.

“Bai kamata ace wanda ya taba rike mukamin minista ya bayyanawa jama’a wani sirri da suka tattauna da Shugaban kasa ba, wannan lamari ba kawai abin bakin ciki da takaici ba ne, har ma da rashin cancanta bisa matsayin da aka ba shi, hakan ya nuni bai kamata a kara aminta da shi ba, wannan dabi’a cin mutunci ne ga shugaban kasa da fadar shugaban kasa. Ya kamata ya fahimci illar abubuwan da ke tattare da bayyanawa mutane sirrin tattaunawa da shugaban kasa, tabbas hakan ta tabbatar da cewa bai ma cancanci zama Minista ba tun da farko”. A cewar Com. Danjuma Gwale

Nan Ba Da Jimawa a Matsalar Ruwa A Tudun Wada Za Ta Zo Karshe – Shugabar Karamar Hukumar

Kungiyar bayyana hirar da Gwarzo ya yi a matsayin wani yunkuri na bata wa Shugaban kasa suna, inda hakan tasa ta gargadin Gwarzo da ya gaggauta janye kalamansa ko su dauki matakan da suka dace akansa.

“A tarihin Nigeria babu wani minista da aka taba cire ya yi abun da T-Gwarzo yayi, Kamata yayi da aka cire shi ya fito ya gode wa Shugaban kasa da ya ba shi damar yin aiki sannan ya ci gaba da harkokin rayuwarsa kamar dai yadda sauran ministocin da Shugaba Tinubu ya cire suka yi. Amma Gwarzo ya fito yana ta kalamai marasa dadi tamkar ma Shugaban kasa ya yi laifi saboda ya yi abun da yake a cikin kundin tsarin mulkin Nigeriya. Inji shi

“Maganganun da ya yi suna iya zama zagon kasa ga shugaban kasa, me ya sa sai yanzu yake baiwa shugaban kasa shawarar ya nada Gawuna, ai kamata ya yi ya fadi hakan tun lokacin da aka nada shi a matsayin Minista a 2023.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...