Shugaba Bola Tinubu na cikin manyan shugabannin da suka isa Riyadh babban birnin Saudiyya domin halartar taron ƙoli na ƙasashen Musulmi da Larabawa.
Taron wanda aka fara ranar Litinin 11 ga watan Nuwamba, zai mayar da hankali ne kan rikicin da ake fama da shi a Gabas Ta Tsakiya.
Tinubu ya samu tarba daga tawagar gwamnatin Saudiyya karkashin jagorancin matamakin gwamnan Riyadh, Mohammed Abdurrahman.
Wata sanarwa da mai bai wa shugaban shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya fitar ta ce Tinubu zai gabatar da jawabi a kan rikicin Isra’ila da Falasɗinawa, inda zai jaddada matsayar Najeriya ta neman sasanta rikicin ta hanyar tsagaita wuta nan take, tare da neman a sake farfaɗo da masalahar samar da ƙasashe biyu masu cin gasin kansu – wato Falasɗinu da Isra’ila.
Ministan yaɗa labarai Mohammed Idris ya ce Najeriya ta halarci taron ne saboda irin daɗaɗɗiyar alaƙa mai kyau da take da ita da yankin na Gabas ta Tsakiya.

“Dole ne mu samar da hanyar diflomasiyya domin warware wannan rikicin, saboda yaƙi ba shi ne mafita ba,” kamar yadda ministan ya faɗa wa manema labarai a birnin Riyadh. “Wannan shi muke buƙata a yi.”
Ya ce Najeriya za ta kuma yi amfani da lokacin taron wajen nema “da babbar murya a idon duniya” buƙatar dukkan ƙasashe su cimma matsaya ɗaya ta warware rikicin Isra’ila da Falasɗinu.
Wata Kungiya ta gargaɗi tsohon Minista Gwarzo ya daina sukar Tinubu saboda cire shi
“Ƙasashen biyu da ke rikici da juna na rasa abubuwa muhimmai, don haka Najeriya na ganin cewa muddin ba a samar da mafita ta diflomasiyya ba, rikicin zai iya shafar ɗaukacin yankin, har ma da duniya baki ɗaya.
Babu yadda Najeriya za ta zauna cikin kwanciyar hankali muddin ba a samu zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya ba,” in ji Idris.
Harin da Hamas ta kai wa Isra’ila ranar 7 ga watan Oktoban 2023 ya janyo mutuwar mutum aƙalla 1,200, da kuma yin garkuwa da kusan 251.
Tun bayan nan, Isra’ila ta kaddamar da mamaya kan zirin na Gaza, inda ta kashe sama da mutum 43,000, waɗanda yawancinsu mata ne da kuma ƙananan yara.
Isra’ila ta sha alwashin ci gaba da farmaki a Gaza har sai ta ga bayan ƙungiyar Hamas da ke iko a Gaza.
Gaza na kuma fuskantar matsananciyar matsalar jinƙai, inda wani rahoto ya yi gargaɗin cewa za a iya fuskantar “mummunan fari” a arewacin Gaza, kuma yaɗuwar rikicin zai iya jefa rabin al’ummar yankin mutum miliyan 2.3 cikin yunwa.