Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Darakta Janar na hukumar kula da ingantuwar aiyuka ta kasa Baffa Babba Danagundi ya sami digirin girmamawa daga wata jami’ar mai suna American Management University da ke birnin London na kasar Birtaniya.
Da yake ba da Digirin girmamawar ga Danagundi da wasu mutane biyar, Dr. Saf Buxy wanda Dr Justina Mutale da Roy Virgen da suka taimaka masa, ya ce an baiwa Danagundi digirin girmamawar ne saboda gudunnawar da yake bayarwa wajen gina rayuwar al’umma, Ilimi da samawa matasa aiyukan yi.
“Tabbas an ba da wannan digirin girmamawar akan lokacin da ya dace.

A matsayinsa na Darakta Janar na hukumar kula da nagartar aiyuka ta kasa, ko shakka babu hakan zai kara masa kwarin gwiwar tabbatar da matasan Nigeriya sun zama masu nagarta.
Jami’ar tana taya ku murna tare da fatan za mu kara samun hadin gwiwa da ku da kuma gwamnatin Najeriya.” Inji Dr Saf Buxy.
Da yake jawabi game da karramawar, Danagundi a madadin sauran wadanda aka karrama sun nuna matukar jin dadinsu ga jami’ar da ta karrama. Ya kuma ba jami’ar tabbacin ci gaba da yin aikin hadin gwiwa ta fuskar ci gaban al’umma da samar da ayyukan yi ga Matasa.
Nan Ba Da Jimawa a Matsalar Ruwa A Tudun Wada Za Ta Zo Karshe – Shugabar Karamar Hukumar
Da yake karin haske ga manema labarai, babban mataimaki na musamman kan harkokin yada labarai ga Darakta Janar Victor Ainoko bayan bikin da aka gudanar a birnin Landan, Ainoku ya ce Danagundi ya tafi ziyarar aiki a birnin Geneva na kasar Switzerland domin halartar taron ƙwadago na kasa da kasa inda aka tattauna muhimman batutuwa.
Ya dawo Najeriya ne a ranar Asabar inda mataimaki na musamman ga shugaban majalisar dattawa Nasiru Usman Naibawa ya tarbe shi a filin jirgin sama a madadin Gamayyar kungiyoyin goyon bayan Tinubu na Arewa maso yamma.
Ainoku ya shaidawa manema labarai cewa gamayyar kungiyoyin goyon bayan Tinibu za su ta shirya liyafar karrama ta musamman ga Danagundi domin ta ya shi murnar wannan karramawar da ya samu.