Daga Rukayya Abdullahi Maida
Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba zai cire wasu mambobin majalisar zartarwa da aka tantance kwazonsu a ƙarƙashin abin da aka tsara su yi.
Gwamna Yusuf, wanda ya tabbatar da karɓar rahoton kwamitin duba aikin mambobin majalisar, ya bayyana cewa jama’a za su ji matakin da gwamnati za ta ɗauka nan ba da jimawa ba.

Mai magana da yawun gwamnan Sanusi Bature Dawakin-Tofa ne ya bayyana haka a ciki wata sanarwa da ya aikowa kadaura24.
Gwamnan ya tunatar da al’umma game da shirin sauya wasu daga cikin mambobin majalisar a wata hira kai-tsaye da aka yi da shi ta gidan rediyo tare da wasu kafofin yada labarai da aka gudanar a Fadar Gwamnati a ranar Laraba.
Gwamnan Kano ya gabatarwa majalisar dokoki kasafin kudin 2025
Ya bayyana cewa rahoton ba zai yi amfani yanzu ba, saboda kasancewarsa tare da su a tsawon shekara ɗaya da rabi ya ba shi damar sanin ƙwarewar su sosai, don haka zai yanke hukuncin karshe game da su da kansa.
Ya bayyana cewa babu ɗaya daga cikin kwamishinonin da suka riƙa neman mukamin, yana mai jaddada cewa kafin naɗin su, ya yi la’akari da ƙwarewa, amana, da kuma shawara daga masu bada shawara.
Ya ce abin da nake buƙata daga kwamishinoni shi ne su kasance masu biyayya gare ni, ga jam’iyyar NNPP, da kuma Tafiyar Kwankwasiyya, tare da jajircewa a kan aikin su da kuma kawo sabbin dabaru don cigaban jihar.