Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya gabatar da kasafin kudin da aka tsara na Shekarar 2025 wanda ya kai Naira N549,160,417,663.00 ga Majalisar Dokokin jihar a ranar Juma’a.
Idan za a iya tunawa kadaura24 ta ruwaito cewa, a kasafin kudin 2024, bangaren ilimi ne ya dauki kaso mafi girma, haka ma a kasafin 2025 , inda aka ware masa N168,350,802,346.19, wanda ya kai kashi 31 cikin dari na jimillar kudin.

Bangaren na ilimi ya samu kashi 29 cikin dari na jimillar kasafin kudin 2024 na Naira biliyan 437.3, amma an dan kara yawan kason a kasafin 2025 da aka tsara.
Zargin cin zarafi: Likitoci sun janye yajin aikin da suka Fara, bayan ganawa da gwamnan Kano
Yayin da yake gabatar da cikakken bayani kan kasafin kudin, wanda aka sanya wa suna Kasafin Fata, Raya Bil Adama da Ci gaban Tattalin Arziki, ga ‘yan majalisar, Mista Yusuf ya bayyana cewa bangaren ayyukan ci gaba na kasafin kudin ya kai N312,634,912,672.18, yayin da aka ware N236,525,504,990.82 ga kudaden kashe-kashen yau da kullum.
Bangaren Masana’antu, Kasuwanci, Kamfanoni da Yawon Bude Ido ya samu kaso mafi karanci na N3,887,338,871.45, wanda ya kai kashi 1.22 cikin dari.