Tsohon ƙaramin ministan gidaje na Najeriya, Abdullahi Tijjani Gwarzo ya ce ya yi mamakin sauke shi da a aka yi daga muƙaminsa.
Yayin wata hira da BBC kwanaki bayan sauke shi , T Gwarzo ya ce babu wani laifi da ya yi, wanda ya janyo aka sauke shi daga muƙamin nasa, sabod a cewarsa ya yi iya baƙin ƙoƙarinsa a muƙamin da aka ba shi.

”Batun ya zo min da mamaki, domin ba na tunanin wani abu mai kama da wannan zai faru da ni”, in ji shi.
Ya ƙara da cewa Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya yi la’akari da tarayyarsu tun ta da can wajen naɗa shi muƙamin.
Gwamnan Kano zai sauya wasu daga cikin kwamishinoninsa
Ya ce fiye da shekara 14 suna tare da Tinubu tun a jam’iyyar ACN, shi da Nuhu Ribadu da Sanata George Akuwam – da ke riƙe da muƙamin sakataren gwamnati a yanzu.
Sai dai ya ce Allah ne ke ba da mulki, kuma ya karɓe a duk lokacin da ya so, don haka ya ce yana gode wa shugaban ƙasar, bisa damar da ya ba shi a gwamnatin tasa.
Ya ce kamata yayi ace da aka cire shi a baiwa wanda ya yiwa jam’iyyar APC takarar gwamnan jihar kano Dr. Nasiru Yusuf Gawuna, indai batu ake na Kano ta tsakiya.
“Amma wanda aka baiwa kujerar bani da wata matsala da shi, kuma Ina yi masa fatan alkhairi, amma wadanda suka kitsa cire ni sun yi maganar siyasa ne”.