Daga Nabahani Yusuf Gogori
Ya mai girma shugaban kasa Ina fata wannan wasiƙar ta same ka cikin koshin lafiya . A daidai lokacin da Najeriya ke cikin wani mawuyacin hali, na rubuto maka wannan wasika ne a yau a matsayina na dan jam’iyyar APC mai kishin kasa da Kano, bisa la’akari da kalubalen da al’ummarmu ke fuskanta da kuma sane da jajircewarka wajen kawar da duk wani kalubale da dora kasar nan a tafarkin tsira .
Amma duk da kokarinka na son hada kan jama’a don cimma nasara, Rikicin cikin gida a jam’iyyar APCn Kano na neman kawo nakasu a ginin da ka yi, wanda hakan tasa na rubuto maka wannan wasika don ka dauki makin da ya dace .
Ya mai girma shugaban kasa, a matsayinka na babban kwamandan Askarawan Nigeria kuma jagoran jam’iyyarmu, a kwai bukatar ka gaggauta daukar matakai don magance matsalolin da ka iya tasowa. Idan ba a kula ba, hakan zai iya rikidewa zuwa rikicin da zai iya haifar da mummunar illa ga jam’iyyar, wanda hakan zai sa jam’iyyar ta fuskanci kalubale. Matakin da zaka dauka akan lokaci zai taimaka wajen magance matsalolin da tabbatar da zaman lafiyar jam’iyyar.
A Kano, kowa yasan cewa Dr. Abdullahi Umar Ganduje, tsohon gwamna kuma shugaban jam’iyyar na kasa a yanzu shi ke jagorantar jam’iyyar mu. Kuma dukkanin yan Jam’iyyar sun amince kuma suna yi masa biyayya yadda ya dace.
Idan zaka iya tunawa Dr. Ganduje ya nuna goyon baya ga takararka ta shugaban kasa, tare da nuna tsantsar sadaukarwa, da tsayawa tsayin daka ba tare da tsoro ko Shakka ba a lokacin zaben fidda gwani na shugaban kasa da Babban zaɓen kasa da aka yi don ya tabbatar ka yi nasara kuma hakan ta samu. To sai dai kuma wasu mutane a halin yanzu suna neman ganin sun haifar da matsala tsakaninka da Shugaban jam’iyyar don ganin an raba shi da mukaminsa.

Yallabai, ya zama wajibi a dora wa mataimakin shugaban majalisar dattawa Barau Jibrin alhakin jefa jam’iyyar APC cikin rikicin tun bayan hawansa kan wannan mukamin. A matsayinsa na gogaggen dan siyasa kuma sanata mai wakiltar Kano ta Arewa tun daga shekarar 2015. Shugabancin Barau Jibrin ya haifar da rarrabuwar kawuna a cikin jam’iyyar, lamarin da yake bukatar a dauki matakin gaggawa domin kaucewa barkewar rikici.
Sakamakon tsige Abdullahi Muhammad Gwarzo daga mukamin minista, jam’iyyar APC na fuskantar rikicin da ba a taba ganin irinsa ba a Kano ta Arewa, tun shekarar 2015. Wannan abun da mataimakin shugaban majalisar dattawa Barau Jibrin ya yi, na barazana ga zaman lafiya jam’iyyar. Don haka a matsayinka shugaban kasa, yana da matukar muhimmanci a magance wannan al’amari cikin kwanciyar hankali kafin ya kara girma.
Zargin cin zarafi: An bukaci Gwamnan Kano ya kori kwamishiniyar jin kai
Tsarin siyasar Barau Jibrin da dangantakarsa da al’umma abin tambaya ne, Amma ya yi amfani da tasirinsa wajen korar T Gwarzo daga mukaminsa na minista. Wannan matakin ya batawa mutane da dama rai, idan aka yi la’akari da irin rawar da Gwarzo ya taka a matsayinsa na dan siyasa mai karamci, mai tawali’u, kuma mai gaskiya. Jama’ar Kano ba su ji dadin wannan mataki ba.
Yana da kyau mai girma shugaban kasa ka sani Barau Jibrin yana yi maka biyayya ne kawai saboda a yanzu Kai ne akan mulki, daga lokacin da ka bar mulki to ba shi ba kai.
Yadda rikicin NNPP Kano ya kara ruruwa yayin da Gwamna Abba ya daina daga wayar Kwankwaso
Domin kwantar da hankulan jama’a da warware rikicin da ke faruwa, ya shugaban kasa ka sake baiwa T Gwarzo mukami. Yin hakan zai magance matsalolin da suka taso a APC da karawa jam’iyyar kima a Kano ta Arewa da Kano baki daya.
Ya mai girma shugaban kasa, domin tabbatar da cewa jam’iyyar APC ta dawo kan turba, yana da matukar muhimmanci a rika ba da fifiko wajen hada kai da kuma la’akari da abin da masu ruwa da tsaki a Kano za su bayar. Wannan yana nufin kaurace wa yanke shawarar da ta shafi mutum daya da ke ikirarin mallakar Kano ta Arewa. A maimakon haka, a samar da tsarin da ya hada da mutunta ra’ayoyi al’umma daban-daban da kuma inganta hadin kai a cikin jam’iyyar.
Yin hakan zai karfa jam’iyyar da kuma nuna kwazonka na ganin ka yi adalci ga kowa. Wannan tsarin zai taimaka wajen hana rigingimu da kuma tabbatar da cewa an biya bukatun jam’iyyar yadda ya dace. Yana da mahimmanci a gane cewa nasarar jam’iyyar ta dogara ne ga hadin kan masu ruwa da tsaki na jam’iyyar ba bukatun mutum daya ba.
Ya kamata ka sani ya mai girma shugaban kasa, ana iya danganta nasarorin zaben da Barau ya samu a matsayin farin jinin ‘yan takarar majalisar wakilai da suka fito daga shiyyarsa. Jama’ar mazabarsu na yaba wa wadannan mutane da kuma girmama su. Sai dai kuma, maimakon yin amfani da karfin nasa, Barau yana dogaro da kyakykyawan fata da kimar wadannan ’yan takara don samun nasarar zaɓensa.
Har yanzu bai makara ba, Shugaban kasa zai iya yin abun da ake bukata don maslahar Jihar Kano da jam’iyyar gaba daya. Bisa la’akari da tarihi, ina roƙon ka da ka tunkari wannan munanar matsalar da ke barazana ga ci gabanmu baki daya.
Nabahani Yusuf Gogori ne ya rubuta wasikar daga garin Gogori a karamar hukumar Bagwai, jihar Kano.