Gwamnan Kano Ka Cire Kwamishiniyar Jin Kai Saboda Za ta Jawo Maka Bakin Jini – Anas Abba Dala

Date:

Daga Buhari Ali Abdullahi

 

Babban Mai taimakawa gwamnan jihar kano na musamman kan wayar da kan al’umma ta fuskar Siyasa Hon. Anas Abba Dala ya roki gwamnan Abba Kabir Yusuf da kori kwamishiniyar ma’aikatar jin kai Hajiya Amina HOD saboda zargin da Ake yi Mata na cin zarafin wata likita.

“Abun da ake zargin kwamishiniyar da shi ba dabi’ar gwamnanmu ba ce , kuma hakan zai zubar da kimar gwamnati da ta gwamnan jihar kano Alhaji Abba Kabir Yusuf Kasance

Anas Abba Dala ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da yayi da jaridar kadaura24 ranar litinin.

Talla

Ya ce akwai bukatar gwamnan jihar kano ta Fara dakatar da ita sannan kasa a binciki lamari, idan har an same ta da laifi sai a hukuntata bayan a koreta daga mukamin kwamishiniya.

“Gwamnan Kano mutum ne mai mutunci da kyamar cin zarafin al’umma saboda hakan ba dabi’arsa ba ce, don haka bai kamata a sami wani daga cikin Jami’an gwamnatinsa da wannan mummunar dabi’ar ba”. Inji Anas Abba Dala

Yadda rikicin NNPP Kano ya kara ruruwa yayin da Gwamna Abba ya daina daga wayar Kwankwaso

Ya ce yana da yakinin gwamnan jihar kano Alhaji Abba Kabir Yusuf zai ba da umarnin bincika wannan al’amari don gano mai gaskiya tare da daukar matakan da suka dace akan mara gaskiya.

Idan za a iya tunawa kadaura24 ta rawaito kungiyar likitoci ta jihar kano ta yi kira ga gwamnan jihar kano Alhaji Abba Kabir Yusuf da ya kori kwamishiniyar ma’aikatar jin kan al’umma bisa zarginta da cin zarafin wata likita a asibitin kwararru na Murtala Muhammad dake Kano.

Sai dai a wani martani da ta yi kwamishiniyar Hajiya Amina Abdullahi HOD ta ce Kiran da likitoci suka yiwa gwamnan Kano na ya cire ta bai firgita ta ba, saboda abun da ya yi ta yi shi ne akan aikinta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bayan tura Kashim ya taho da gawar Buhari, Tinubu ya ba da umarnin sassauta Tutar Nigeria

Shugaban kasa Bola Tinubu ya bada umarnin ayi kasa...

Yanzu:yanzu: Tsohon shugaban Nigeria Buhari ya rasu

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un!!! Allah yayi wa tsohon shugaban...

Tinubu ka fadawa yan Nigeria Inda ka tsaya har kwana 5 bayan taron BRICS – ADC

    Jam'iyyar African Democratic Congress wato ADC ta soki Shugaban...

Da dumi-dumi: Yadda akai Jami’an tsaro suka kama ni -Danbello

Rahotannin sun tabbatar da cewa jami'an tsaro a Nigeria...