Zargin cin zarafi: An bukaci Gwamnan Kano ya kori kwamishiniyar jin kai

Date:

Ƙungiyar Likitoci ta ƙasa reshen jihar Kano ta yi kira ga Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya gaggauta korar Kwamishiniyar Jin Kai da Walwalara Jama’a ta jihar Hajiya Amina Abdullahi wato Amina HOD nan da awanni 48 bisa zarginta da cin zarafin wata likita.

Shugaban Kungiyar Dr. Abdurrahman Ali ya shaida wa Freedom Radio cewa suna zargin Kwamishiniyar da cin zarafin wata likita Dr. Nusaiba Mahmud a lokacin da take tsaka da aikinta a sashen bada agajin gaggawa na ɓangaren yara na Asibitin Murtala a ranar Jumu’ar da ta gabata.

Talla

A wani bidiyo da likitar ta fitar ita ma ta bayyana yadda ta sha da ƙyar inda ta ce, Kwamishiniyar ta haƙiƙi ce tana iƙrarin cewa koda ita ƴar Gwamnan Kano Engr. Abba Kabir Yusuf ce to sai ta ɗanɗana kuɗarta.

An Kuma: Wani Dan Majalisar NNPP Kano ya sake ficewa daga Kwankwasiyya

Game da wannan zargi Freedom Radio ta tuntubi Kwamishiniyar Jin Kan ta Kano Hajiya Amina HOD amma koda aka soma yi mata bayani ta wayar tarho sai ta kashe wayar, daga nan muka sake kiranta amma an saka wayar a ‘Forward”, hakan ce ta sa muka aika mata da sakonnin kar-ta-kwana amma har kawo lokacin da muke hada wannan rahoton bata amsa ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin Sarautar Kano: Fadar Sarki Sanusi ta zargi magoya bayan Sarki Aminu Ado Bayero da kai farmaki Kofar Kudu

Daga Sani Idris Maiwaya   Rikicin Masarautar kano ya na neman...

Shugabannin Kasuwar Kanti Kwari sun shiryawa Gwamnan Kano Addu’o’i na musamman

Daga jafar adam Shugaban kasuwar Kantin Kwari Sharu Abdullahi Namalam...

Dalilin Kwankwaso na kin shiga Hadakar ADC

Jam'iyyar NNPP ta ce abin da ya sa ba...