Yadda rikicin NNPP Kano ya kara ruruwa yayin da Gwamna Abba ya daina daga wayar Kwankwaso

Date:

Daga Sharifiya Abubakar

 

Rikicin da ya barke a jam’iyyar NNPP, a Kano, ya fara yin kamari, sakamakon yadda Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya ki halartar wasu taruka, ya kuma ya ki daga kiran wayar da ubangidansa, Rabiu Kwankwaso ya yi masa, kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta rawaito.

Lamarin ya Fara kamari ne tun lokacin da wata kungiyar mai suna “Abba tsaya da kafarka” ta bulla, wadda kuma take kara samun karbuwa a ciki da wajen jam’iyyar NNPP.

Kadaura24 ta rawaito cewa rikicin siyasar Abba Kabir ya rabu da ubangidansa Kwankwaso an kaddamar da shi ne ta bangarori daban-daban.

Talla

Ana ganin wasu daga cikin jiga-jigan jam’iyyar NNPP suna tattaunawa da jam’iyyar APC, wasu kuma tuni suka samo umarnin kotu na karbe ikon jam’iyyar NNPP daga hannun Kwankwaso.

Idan za a iya tunawa a ranar 1 ga Nuwamba, wata babbar kotun jihar Abia ta yi hukuncin cewar ta mayar da ikon jam’iyyar NNPP ga tsohon shugaban jam’iyyar, Boniface Aniebonam.

Masana harkokin Siyasa na ganin an kai rikicin NNPP Kotu ne don a haifar da bangaranci a cikin jam’iyyar da kuma sharewa gwamnan da wasu yan majalisa fage don sauya sheka zuwa APC.

An Kuma: Wani Dan Majalisar NNPP Kano ya sake ficewa daga Kwankwasiyya

Manya daga cikin wadanda ake ganin Rikicin ya fi kamari akan su sune: sakataren gwamnatin jihar, Baffa Bichi; kwamishinan sufuri na jihar, Mohammed Diggol; kwamishinan ilimi na jihar, Umar Doguwa; Sanata mai wakiltar Kano ta Kudu, Kawu Sumaila; da dan majalisar tarayya mai wakiltar Rano/Bunkure/Kibiya.

Wasu yan cikin gida a Kwankwasiyya sun shaida wa Daily Nigerian cewa gwamnan ya riga ya saurari kiraye-kirayen da aka yi masa na cewa ya zama mai cin gashin kansa daga hannun Kwankwaso domin sami damar gudanar da gwamnatinsa da kansa.

“Abba baya son bijirewa Kwankwaso, amma da gaske yana son ya tsaya da kafarsa. Kashi 90 cikin 100 na kwamishinonin Kano Kwankwaso ne ya dora su, kuma har yanzu Abba yana aiki da su. Wannan ya nuna har yanzu yana girmama shi.

Abba ya dade yana so ya sauke wasu daga cikin kwamishinoninsa wadanda ko dai ba sa Aikinsu yadda ya dace ko kuma ba sa yi masa biyayya, amma saboda girmama Kwankwaso ya hana su karbar su domin a samu zaman lafiya.” Inji wani makusancin gwamnan.

A cewar majiyoyi, gwamnan ya koka da yadda ubangidansa ke yin katsalandan a harkokin gwamnatin Kano musamman a harkokin da suka shafi kananan hukumomi.

DAILY NIGERIAN ta ce ta sami labarin cewa rikicin da ya fara kunno kai ne tun a watan Maris din wannan shekara, lokacin da Kwankwaso ya nada shugabannin riko na kananan hukumomin Kano shi kadai ba tare da baiwa gwamna Abba Kabir Yusuf dama ko daya ba.

Idan za a iya tunawa kadaura24 ta rawaito a ranar Lahadin da ta gabata ne mamba mai wakiltar karamar hukumar Dala a majalisar tarayya Ali Madaki da takwaransa na Rano Kibiya da Bunkure Kabiru Alhassan Rurum suka bayyana ficewarsu daga tafiyar Kwankwasiyya tare da yin kira ga dukkan magoya bayansu da su ajiye jar hula, Sannan suka bayyana biyayyarsu ga gwamnan Kano har suka yi kira a gareshi da ya tsaya da kafarkarsa.

Haka kuma ana sa ran karin ‘yan majalisar NNPP za su fito fili su yi watsi da tafiyar Kwankwasiyya tare da yin mubayi’a ga sabuwar tafiyar “Abba tsaya da kafarka”.

Zargin cin zarafi: An bukaci Gwamnan Kano ya kori kwamishiniyar jin kai

Daily Nigerian ta rawaito cewa majiyoyin da ke da masaniya kan lamarin sun ce a cikin ‘yan majalisar dokokin jihar 26 na jam’iyyar NNPP, wakilai uku ne kawai masu wakiltar Madobi, Nassarawa da Kiru ba sa cikin kungiyar “ Abba Tsaya da Kafarka”.

Kokarin jin ta bakin Kwankwaso ya ci tura, amma wasu majiyoyi na kusa da shi sun zargi gwamnan da jagorantar yiwa ubangidansa na siyasa tawaye tare da daukar nauyin Kungiyar Abba tsaya da kafarka.

“Kwankwaso yana da nasa matsalolin a matsayinsa na mutum, amma bai cancanci wannan abun ba. Domin Abba ya zama Gwamna, Kwankwaso ya raba gari da babban amininsa Aminu Dabo, da kuma manyan makusantan siyasarsa irin su Rabiu Sulaiman Bichi, Yunusa Dangwani da Yusuf Bello Dambatta,” inji majiyar da ke biyayya ga Kwankwaso.

Mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Dawakintofa, ya ki cewa komai kan lamarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...