An Kuma: Wani Dan Majalisar NNPP Kano ya sake ficewa daga Kwankwasiyya

Date:

Daga Halima Musa Abubakar

 

Dan majalisar tarayya mai wakilar kananan hukumomin Rano Kibiya da Bunkure Kabiru Alhassan Rurum ya bayyana cewa daga yau ya fice daga Kwankwasiyya tare da ajiye jar hula.

“Sakamakon hukuncin da babbar kotun Jihar Abia ta yi na tabbatarwa da ainihin mau Jam’iyyar NNPP a kasa Dr. Boniface Aniebonam Jamiyyar sa, daga yau Lahadi 3 ga watan Nuwambar 2024, Ni RT. Hon. Kabiru Alhassan Rurum na yarda da hukuncin da wannan Kotu ta yi Kuma ina tare da mai Jam’iyyar Dr Boniface Aniebonam a Jam’iyyar NNPP me kwandon kayan Marmari”. Inji sanarwa

Talla

Wannan saƙo na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai mai ɗauke da sa hannun mai taimakawa Hon. Kabiru Alasan Rurum a harkokin yaɗa labarai Fatihu Yusuf Bichi.

Haka Kuma daga wannan rana na ajiye jar hula kuma ina tare da mai girma gwamnan Jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf.

Dan majalisar tarayya na NNPP daga Kano ya fice daga Kwankwasiyya

” Ina kira ga gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf da ya TSAYA DA KAFARSA dan ya samu damar sauke nauyin da Allah ya dora masa da Kuma Al’ummar jihar Kano da suka zabeshi.

Idan za a iya tunawa kadaura24 ta rawaito a yammacin wannan rana ta lahadi dan majalisar tarayya mai wakilar karamar hukumar Dala Aliyu Sani Madakin Gini ya bayyana ficewarsa daga tafiyar ta Kwankwasiyya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Abubakar Bichi ya bada gudumawar motocin bas 13 ga jami’o’in Kano da taraktoci 11 ga yan mazabarsa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu Dan Majalisar tarayya mai wakiltar karamar...

Rikicin Sarautar Kano: Fadar Sarki Sanusi ta zargi magoya bayan Sarki Aminu Ado Bayero da kai farmaki Kofar Kudu

Daga Sani Idris Maiwaya   Rikicin Masarautar kano ya na neman...

Shugabannin Kasuwar Kanti Kwari sun shiryawa Gwamnan Kano Addu’o’i na musamman

Daga jafar adam Shugaban kasuwar Kantin Kwari Sharu Abdullahi Namalam...