Daga Zainab Muhd Darmanawa
Karamar hukumar Kumbotso ta kaddamar da wasu jami’an kula da tsaro guda 100 da suka hadar da ‘yan sintiri da mafarauta a yunkurin ta na inganta tsaron yankin.
Kadaura24 ta rawaito Shugaban karamar hukumar, Alhaji Garban Kauye Farawa ne ya sanar da hakan, yayin gudanar da wani taron masu ruwa da tsaki akan al’amuran tsaro a yankin, yana mai karawa da cewa kowanne daga cikin jami’an zai rika karbar kudaden alawus na Naira dubu 20 kowanne wata.
Farawa ya kuma kara da cewa karamar hukumar zata ginawa jami’an ofishi na din-din-din, a daidai lokacin ya mikawa ofishin ‘yan sanda na unguwar Ja’o’ji sabuwar motar sintiri kirar Sharon Domin inganta tsaro a yankin.
Hakazalika farawa ya Raba sababbon mashi nan hawa guda 10, inda ya baiwa jami’an Sintiti na Vigilante Sabon babur 5, kirar CIB 1, kwamandan Hisba Kuma an bashi 1, DSS 1, mafarauta 1, sai Kuma jami’an yan sanda da Suma suka Rabauta da guda 2 Domin fadada Harkar Sintirinsu da tsaro a Karamar Hukumar.
Cikin wata sanarwa dauke dasa hannun Mai Taimakamasa Kan harkokin yada labarai Shazali farawa ya Rawaito cewa, a nasa bangaren mai martaba sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, wanda ya samu wakilcin Hakimin Kumbotso, Alhaji Ahmad Ado Bayero ya bada tabbacin cewa dukkannin masu rike da sarautun gargajiya a yankin, zasu bada gudunmawar data dace wajen kare lafiya da dukiyoyin al’umma, tare da yabawa Shugaban karamar Hukumar bisa wannan namijin kokari.
קמגרה תשדרג לכם את חיי המין ותאפשר לכם הנאה מרבית מהאקט. לטבע פלז’ר שלל פתרונות טבעיים נוספים שישדרגו לכם את חדר המיטות. מכוני ליווי
קמגרה למכירה במודיעין פעמים רבות אנחנו יודעים שאנחנו צריכים לעשות משהו, אבל “רק הפעם” פשוט נמנעים מלעשות את זה, פשוט כי זה דורש יותר מדי מאמץ. אותו הדבר נערה ליווי