Mun Dakatar da Fafutikar Neman Tsige Ganduje daga shugabancin APC – Matasan Arewa ta tsakiya

Date:

Gamayyar kungiyoyi matasan Arewa ta tsakiya  ta ce ta dakatar da fafutikar da ta ke yi ta neman tsige Dr.Abdullahi Umar Ganduje daga matsayinsa na shugabancin jam’iyyar APC.

Shugaban gamayyar kungiyoyin, Hon Abdullahi Sale Zazzaga ne ya bayyana hakan a wata hira da yayi da manema labarai a ranar laraba.

Talla

Zazzaga ya ce manyansu ne su ka ja hankalinsu dan su dakatar wannan fafitika musamman duba da cewar taron kwamatin zartarwa na jam’iyyar na karatowa.

Zazzaga ya ce, “komai da kaga ana yi ana yine bisa dalili. Muna siyasa dan neman yanci ne kuma bisa doron dalili.

Rikicin NNPP: Gwamnan Kano ya Bijirewa Umarnin Kwankwaso, na cire wasu jami’an gwamnati

Dalilin kuma shi ne domin cigaban yankinmu da al’umarmu da zaman lafiyar su da kuma bunkasar tattalin arzikinsu.

Talla

“Abinda ya faru shi ne, mun yi fafutika,kowa da yake fadin kasarnan ya san mun yi fafitika,kuma ba daina fafitika za mu yi ba.

“Muna wannna fafitika ne saboda ci gaban al’umma,amma sai dai komai da mu ke yi muna da manya. A cikin wannan tafiya da mu ke yi manyanmu sun kiramu sun zauna damu, kuma sun ce lokaci ya yi da za mu tsaya da wannnan fafutika saboda duk wanda ya kamata ya jimu ya jimu, wanda yakamata ya yi magana ya yi magana, sun umarce mu da dakatar da wannan fafitika tun da taron kwamatin zartarwar na jam’iyyar na karatowa nan da kwanaki.

Talla

“Sun ce mu jira muga me kwamatin zai yi akai, duk abin da NEC ta yanke daga nan sai mu san mu san matakin da za mu dauka na gaba.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Inganta Noma: Sanata Barau zai tallafawa Matasa 558 daga Arewa maso yammacin Nigeria

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...

Kwamitin Majalisar Wakilai ya gabatar da shawarar kara Jihohi 31 a Nigeria

Daga Maryam Muhammad Ibrahim Kwamitin majalisar wakilan Nigeria mai kula...

Sarkin Kano na 15 ya gana da Shugaba Tinubu kan rikicin Rimin Zakara

    Mai Martaba Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado...

Da dumi-dumi: Tinubu ya baiwa sakataren jam’iyyar APC na Kano mukami

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Sakataren jam’iyyar APC na jihar Kano,...