Rikicin PDP: Gwamnonin PDP sun bayyana Matsayarsu

Date:

Daga Rahama Umar Kwaru

 

Gwamnonin babbar jam’iyyar adawa a Najeriya ta PDP sun soke dakatarwar da aka yi wa muƙaddashin shugaban jam’iyyar na ƙasa, Iliya Damagum.

Gwamnonin sun kuma soke dakatarwar da aka yi wa sakataren hulɗa na ƙasa na jam’iyyar, Debo Ologunagba, da mai ba da shawara kan harkokin shari’a, Kamaldeen Ajibade.

Wannan na kunshe ne cikin jawabin da shugaban gwamnonin jam’iyyar kuma gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya yi wa manema labarai a safiyar yau Talata.

Bala ya ce Damagum ne shugaban jam’iyyar da suka sani yanzu kuma shi zai ci gaba da riƙe kujerar.

Tun da farko dai, wani ɓangaren kwamitin zartaswar jam’iyyar na ƙasa da ya ɓalle ya sanar da naɗa Yayari Mohammed a matsayin wanda zai maye gurbin Damagum, inda kowane ɓangare ya yi iƙirarin dakatar da ɗayan.

Talla

A wata sanarwa ranar Lahadi, Yayari ya ce kwamitin zartaswar jam’iyyar ya naɗa shi ne domin mayar da dawo da jam’iyyar kan turba.

Ya ce PDP ba ta yin adawa yadda ya kamata saboda kowa ya ɗora buƙatar kansa a gaba kafin ta jam’iyya – musamman ma wasu jagororin kwamitin na zartaswa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Sarkin Kano na 15 ya gana da Shugaba Tinubu kan rikicin Rimin Zakara

    Mai Martaba Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado...

Da dumi-dumi: Tinubu ya baiwa sakataren jam’iyyar APC na Kano mukami

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Sakataren jam’iyyar APC na jihar Kano,...

Gwamnatin Kano ta haramtawa yan kwangila zuwa ma’aikatar kananan hukumomi ta jihar – Kwamishina

Gwamnatin kano ta ja kunnen yan kwangilar ayyukan kananan...

Iftila’i: Almajirai 17 sun kone kurmus 15, sun jikkata sanadiyya wata gobara

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Wata gobara da ta tashi ta...