Daga Aliyu Danbala Gwarzo
Gwamnan jihar kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya ba da umarni ga shugabannin riko na kananan hukumomi 44 dake jihar Kano da sauka daga mukamin da ya basu.
Gwamnan ya bayyana hakan ne lokacin da ya gana da shugabannin rikon a gidan gwamnatin jihar kano a ranar larabar nan.
Gwamnan ya kuma umarci shugabannin rikon da su mika ragamar mulki nan take ga manyan ma’aikatan gwamnatin dake kananan hukumominsu wato (DPM).
Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar kano ta sanya ranar asabar 26 ga watan October, 2024, domin gudanar da zaben kananan hukumomi a fadin jihar Kano.