Kotu ta tsayar da ranar da za ta yanke hukunci kan karar da ke neman tsige Ganduje a matsayin Shugaban APC

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta sanya ranar 23 ga watan Satumba, 2024, domin yanke hukunci kan karar da ake neman tsige Dr Abdullahi Ganduje a matsayin shugaban jam’iyyar APC na kasa.

Idan dai za a iya tunawa, a zaman da aka yi a baya a ranar 5 ga watan Yuli, alkalin kotun, Mai shari’a Inyang Ekwo, ya sanya ranar Laraba, 18 ga watan Satumba, a matsayin ranar yanke hukunci kan karar, amma kuma sai ba a sanya karar cikin jerin kararrakin da aka karanta a yau ba.

‘’ Da aka gudanar da bincike, an bayyana cewa ba a kammala hukuncin ba, kuma tun da farko magatakardar kotun ta sanar da wadanda ke cikin karar dalilin dage ranar.

EFCC ta ce Yahaya Bello ba ya hannunta

“Tuni mun kira wadanda suke cikin karar ta wayar tarho domin sanar da su ci gaban da aka samu. Sabuwar ranar da aka sanya ita ce 23 ga watan Satumba 2024″ kamar yadda aka bayyana.

Kungiyar APC ta Arewa ta tsakiya karkashin jagorancin Saleh Zazzaga, ta shigar da kara ne ta hannun lauyansu, Benjamin Davou, inda suka kalubalanci yadda aka nada Ganduje a matsayin shugaban jam’iyyar APC a lokacin da ya kamata ace dan shiyyar Arewa ta tsakiya ne yake jagorantar jam’iyyar.

A cikin karar mai lamba: FHC/ABJ/CS/599/2024, sun yi fatan kotun ta hana Ganduje bayyana kansa a matsayin shugaban jam’iyyar APC.

Nema yafiya:Bafarawa ya baiwa mutanen sokoto Naira Biliyan 1

Sun yi ikirarin cewa kwamitin zartaswar jam’iyyar APC na kasa ya saba wa kundin tsarin mulkin jam’iyyar ne a lokacin da ya nada Ganduje daga jihar Kano a shiyyar Arewa maso Yamma, ya maye gurbin Sen. Abdullahi Adamu daga jihar Nasarawa a shiyyar Arewa ta tsakiya.

Sun kuma kara da cewa nadin da aka yiwa Ganduje na maye gurbin Abdullahi ya sabawa doka ta 31.5(1) f na kundin tsarin mulkin jam’iyyar APC .

Wadanda suka shigar da karar sun yi ikirarin cewa, Ganduje yana rike da ofishin shugaban jam’iyyar APC ne ba bisa ka’ida ba, kasancewar ba dan jihohin dake shiyyar Arewa ta tsakiya ba.

Masu shigar da karar sun ambaci Ganduje, APC, da kuma hukumar zabe mai zaman kanta, a matsayin wadanda ake kara na 1 zuwa na 3 a karar.

Solacebase

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dr. Kabiru Getso Ya Mika Ta’aziyya Ga Iyalan Buhari

Daga Rahama Umar Gwaru   Tsohon kwamishinan ma'aikatun lafiya da muhalli...

Gwamnatin tarayya ta ayyana Ranar hutu saboda rasuwar Buhari

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ayyana Talata, 15 ga watan...

Injiniya Iliyasu Usman Salihu ya zama Jakadan zaman Lafiya na Africa

    Injiniya Ilyasu Uasman Salihu, Manajan Darakta na Sadex Engineering...

Halin da ake ciki game da shirye-shiryen jana’izar Buhari

Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda, ya bayayna cewa sai...