Warwarar zare da abawa kan dambarwar NNPCL da matatar mai ta Dangote

Date:

 

Kamfanin mai na ƙasa NNPC shi ne ya yi wannan warwarar zare da abawar, tare da fito da wasu muhimman Abubuwa da suka faru ko suke faruwa tsakaninsa da matatar mai ta Dangote.

1- Gwamnatin tarayya ko NNPC Ltd, ba su suka Kara Farashin man fetur ba.

2- A wannan yanayi da ake ciki, kasuwa ce ke halin ta dangane da farashin man fetur

3- Ba shi yiwuwa Dangote ya sai da man sa a faduwa, tunda farashin gangar mai ya zarce Dala 70 a kasuwar duniya.

4- A yanzu haka, a kan Naira 898 duk Lita Kamfanin NNPC Ltd ke sayan fetur daga matatar Dangote.

Bayan sauke Kantomomin kananan hukumomin, gwamnan kano ya bayyana wadanda za su mikawa ragamar

5-Akwai yarjejeniya tsakanin NNPC Ltd da Dangote, inda zai rinka samar da Lita miliyan 25 duk Rana, Wanda zai fara daga ranar 15 ga watan Satumban 2024.

6- A ranar Asabar 14, ga watan Satumban 2024 Dangote ya rubuto wasika cewa shi Lita Miliyan 16 kacal zai rinka samarwa. Sabanin Lita Miliyan 25 din da aka amince a yarjejeniyar. Ka ga za a samu gibin Lita Miliyan 8.2

7- Daga ranar da aka yi yarjejeniya cewa Matatar man Dangote zata fara ba da fetur ranar 15 ga watan Satumban 2024 har ya zuwa17 ga watan Satumban, Lita Miliyan 5.8 kacal Dangwate ya samar. Wannan na nufin a cikin Lita Miliyan 50 da ya kamata Dangote ya samar na kwanakin biyu, an sami gibin Lita Miliyan 44.2 wanda zai ba NNPC Ltd.

8-Bayan NNPC Ltd ya riga ya bayarda wasikar lamuni (wato Letter of Credit) na biyan Matatar Dangote kudin Lita miliyan 25 duk Rana.

Iftila’i: Yara hudu sun mutu a cikin firinji

9- Tun daga bara kudin da ake sauke man fetur a Najeriya ya kai Naira 1,100. Amma NNPC Ltd ke cike gibin, don jama’ar Najeriya su rinka samun Mai akan Naira 620 duk Lita, kuma a rahusa.

10- Har Saida ta Kai NNPC Ltd ya fito ya baara, sakamakon gano cewa gibin fa da yake cikewa don jama’ar Najeriya su samu fetur cikin rahusa, ya yi yawa.

11- Ba gaskiya bane cewa Gwamnati ce ta kayyade yadda Dangote zai saida Mai. Dangwate shi ne da kansa ya sa Farashin fetur dinsa yake saidawa NNPC Ltd akan Naira 898 duk Lita. Abi sananne cewa tun farko ma sama da naira 900 Dangwate ya so ya siyar da fetur dinsa duk Lita. Sai da NNPC Ltd ta sa baki sannan Dangwate ya dawo da shi Naira 898 duk Lita.

12- NNPC Ltd ya bukaci Dangote ya saidawa sauran dillalan man fetur in har suna bukata.

13- Babban dalilin da yasa NNPC Ltd ke sayen Mai wajen Dangote shine don tabbatarda Yan Najeria na sayen fetur a farashi Mai sauki.

14- Ba gaskiya sam sam batun cewa wai Dangote ya so ya saida man fetur dinsa akan Naira 600 amma wai Gwamnati ce ta kara farashin. Tunfarko Dangwate ya so ya saida man fetur din sa ne akan kudi sama da Naira 900 amma NNPC Ltd ya dage sai ya sayar kasa da haka (wato Naira 898).

Ku lura da kyau, Yan Najeriya!

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi: Tinubu ya Iso Kano domin ta’aziyyar Dantata

Shugaban Nigeria Bola Ahmad Tinubu ya iso jihar Kano...

ALGON ta Kano Sa’adatu Soja ta sami sabon matsayi a kungiyar ALGON ta Ƙasa

Daga: Aliyu Danbala Gwarzo. Shugabar karamar hukumar Tudunwada kuma ALGON...

Da dumi-dumi: Tinubu zai zo Kano

Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu zai zo Kano ranar...

Tinubu ya sauya sunan jami’ar Maiduguri zuwa Sunan Muhd Buhari

Shugaba Bola Tinubu ya sauya sunan Jami'ar Maiduguri zuwa...