Ambaliyar Maiduguri: A hukumance NEMA ta fitar da adadin mutanen da suka rasu

Date:

 

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya, NEMA ta ce kimanin mutum 37 ne suka mutu sakamakon mummunar ambaliya ruwa da ta auka wa birnin Maiduguri.

Yayin zantawarta da BBC shugabar hukumar Hajiya Zubaida Umar ta ce akwai fargabar ƙaruwar waɗanda iftila’i ya shafa, yayin da ma’aikatan hukumar ke cigaba da aikin ceto waɗanda suka maƙale.

Hajiya Zubaida ta kuma ce fiye da mutum 400,000 suka rasa muhallansu sakamakon bala’in.

Asibitin Best Choice Ya Kaddamar Da Sabuwar Na’urar Jarirai Ta (Jaundice) Irinta Ta Farko A Arewacin Najeriya

Shugabar hukumar NEMAn ta kuma bayyana ambaliyar a matsayin mai tayar da hankali.

“Abin akwai tashin hankali, don ruwa ya cinye garin Maiduguri ba kaɗan ba, ga mutane nan kana gani an koro su daga gidajensu”, in ji ta.

Ta ce ambaliyar ta cinye kusan kashi 40 cikin 100 na birnin Maiduguri.

Da dumi-dumi: Rarara Ya Dauki Nauyin Aikin Wani Titi a Jihar Kano

Hajiya Zubaida ta ce har kawo yanzu akwai mutanen da ba a iya ceto su ba bayan da suka maƙale cikin ɓaraguzan gine-gine.

Ta ƙara da cewa jami’an hukumar na ci gaba da aikin ceto mutanen da ambaliyar ta rutsa da su.

”Yanzu haka da nake magana jami’an hukumarmu a cikin unguwanni domin ci gaba da zaƙulo mutanen da har yanzu ke maƙale cikin gidajen da ruwa ya cinye”, in ji shugabar hukumar ta NEMA

Tuni da gwamnan jihar Babagana Umara Zulum ya ce fiye da mutum miliyan guda ne ambaliyar ta shafa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...

Dan majalisa Bichi ya sake biyan kuɗin makarantar dalibai 121 masu karatun digiri na biyu da na digirin digirgir

Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Bichi a Majalisar...