Gwamnatin tarayya ta fara sayar da shinkafarta akan Naira 40,000

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Gwamnatin tarayya ta fara rabon Shinkafar da za ta sayar akan farashi mai sauki,wanda adadinta ya kai ton 30,000 .

Shirin wanda ministan noma da samar da abinci Sanata Abubakar Kyari ya kaddamar, na samar da shi ne da nufin samar da sauki ga ‘yan Najeriy sakamakon tsadar rayuwa da ake fuskanta a kansar tun bayan janye tallafin man fetur.

Za dai a rika sayar da buhunan shinkafar Mai girman 50kg a kan kudi ₦40,000.

Man Fetur shi zai rika yiwa kansa farashi yanzu a Nigeriya – NNPC

Yayin taron kaddamar da shirin a Abuja, Kyari ya jaddada cewa wannan tallafin abinci wani muhimmin bangare ne na kokarin da shugaba Bola Tinubu ke yi na ganin babu wani dan Najeriya da ya kwana da yunwa. Shirin wanda aka tsara shi da gaskiya, za a raba shinkafa a duk fadin kasar, inda ake bukatar masu saye su gabatar da Lambar Shaidar katin dan Kasa (NIN) da lambobin wayarsu domin tantancewa.

 

“Wannan shiri ya zo kan lokacin da ya dace, duba da irin kalubalen da muke fuskanta a kasa baki daya,” in ji Kyari, yana mai cewa shirin sayar da shinkafar har miliyan 30,000 ana sa ran zai taimaka wajen daidaita farashin shinkafa da sauran kayan abinci.

Yanzu-yanzu:Kotu ta baiwa hukumar zaben Kano umarni Kan zaben kananan hukumomi

Ya ce za a sanya idanu sosai a raba shinkafar don tabbatar da cewa wadanda aka yi tsarin don su sun amfana musamman mutane masu karamin karfi da ma’aikatan gwamnati.

Domin tabbatar da gudanar da rabon Shinkafar cikin kwanciyar hankali, gwamnati ta samar da wuraren sayar da ita da dama a fadin babban birnin tarayya da sauran jihohi

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kungiyar ’Yan Jaridun Kano Arewa ta Aike da Sakon Ta’aziyyar Rasuwar Alhaji Aminu Dantata

  Kungiyar ’Yan Jarida ta Kano Arewa ta bayyana alhinin...

Ku na da rawar takawa wajen inganta Lafiyar al’ummar Kano – Waiya ga jami’an yada labarai

Daga Abubakar Sayeed Kwamishinan Ma'aikatar yada labarai da harkokin cikin...

Ana daf da yin jana’izar Aminu Dantata a Madina

Tawagar da gwamnatin Najeriya ta tura zuwa Madina na...