Man Fetur shi zai rika yiwa kansa farashi yanzu a Nigeriya – NNPC

Date:

Daga Aliyu Danbala Gwarzo

 

Kamfanin mai na Najeriya NNPC ya bayyana cewa man fetur a ƙasar shi da kansa ne zai rika yiwa kansa farashi a kasuwa.

Mataimakin shugaban sashin hako mai na kamfanin Mista Adedapo Segun ne ya bayyana hakan yayin wata ganawa da shi a wani Shirin na gidan talabijin na TVC ranar alhamis.

Ya ce kundin tsarin mulki bai ƙayyade waɗanda za su tsayar da farashin man fetur ba.

Yaki da cin hanci: Kungiyar mata Yan jarida ta karrama Muhuyi Magaji

A cewarsa, sashi na 205 da ya kafa kamfanin, ya bashi damar sakin fetur don nemawa kansa farashi a kasuwa.

Ya ƙara da cewa dangane da tsadarsa da mutane ke kokawa, batu ne da ya shafi chanjin kudaden kasashen waje.

” Ba wani mai lafiyayen hankali da zai ji dadi saboda tsadar man fetur kawai ba yadda zamu yi ne, yanzu ba mu da ikon ƙayyade farashin man fetur a Nigeria”.

Amma ya ce su na ƙoƙarin su da dilallan man na ƙasa don ganin an magance karancinsa.

Kungiyar One Voice Initiative ta nada sabbin shugabanninta na kasa

Kuma ya sake tabbatarwa da ƴan Najeriya cewar, nan da kwana ƙalilan za a kawo ƙarshen matsalar ƙarancin man baki ɗaya.

Dan gane da batun man fetur na matatar Ɗangote kuwa, Segun ya ce nan da 15 ga watan satumba za a Fara ganin man a kasuwa kamar yadda aka tsara.

A cewar kamfanin, a halin yanzu man fetur na nemawa kansa farashi ne a kasuwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamna Abba Ya Sanya Hannu Kan Dokar Kafa Gaya Polytechnic

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sanya...

Sojoji sun mikawa Tinubu Shawarwari yadda za a kawo karshen matsalar tsaron Nigeria

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya karɓi rahoton dakarun sojan...

Shugaba Tinubu ya sake nada Buba Marwa a matsayin shugaban NDLEA

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sake tabbatar da nadin...

Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa Ya Koma Jam’iyyar APC a Hukumance

Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar...