Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja karkashin jagorancin mai Shari’a Emeka Nwite, ta bukaci hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar da ta dakata daga karbar Naira miliyan 10 ga masu takarar shugabannin kananan hukumomin da Naira miliyan 5 ga masu takarar kansilolin a zabe mai zuwa.
Idan za a iya tunawa kadaura24 ta rawaito cewa a kwanakin baya, hukumar zaben ta sanya Naira miliyan 10 ga yan takarar kujerun ciyamomi da naira miliyan 5 ga masu takarar kujerun kansilolin a zaɓen da za’a a gudanar a watan gobe.
‘Yan arewa ku yi mana aikin gafara, mun gaza kare ku – ACF
Tun a wancan lokacin ne dai al’umma sukai ta kokawa game da kudin, amma hukumar ta ce ta sanya kuɗin da yawa ne saboda halin da tattalin arzikin kasa yake ciki.
Jam’iyyun SDP da APP da ADP ne dai suka shigar da karar, inda suka kalubalanci kudaden da hukumar KANSIEC ta sanya, sakamakon yawan da suka yi.
Barr. Hassan Tanko kyaure ne dai ya shigar da karar a madadin jam’iyyun guda uku, Kuma shi ne zai tsaya musu a gaban Kotun.
Iftila’i: Rushewar gini ta yi sanadiyar rasuwar mutane 2 a Kano
Kotun ta ce kada hukumar ta sake ta karɓi ko sisin kobo a hannun masu shiga takara har sai ta saurari kundarin Shari’ar.
Kotun dai ta sanya ranar 25 ga watan satumba na wannan shekarar a matsayin ranar da zata saurari kundarin Shari’ar.