Gwamnatin Sokoto ta yi martani Kan batun gyaran burtsatse akan sama da Biliyan 1

Date:

Gwamnatin jihar Sokoto ta ce ta kashe naira biliyan 1.2 wajen aikin tona sabbin rijiyoyin burtsatse masu amfani da hasken rana, ba wai gyara su ba, kamar yadda ake yaɗawa a shafukan sada zumunta.

A baya-bayan wani bidiyon gwamnan jihar, Ahmad Aliyu, ya ɓulla a shafukan sada zumunta, inda yake jawabi a wani wuri da ake kyautata zaton ƙaramar hukumar Wurno ne, yana cewa gwamnatinsa ta kashe naira biliyan 1.2 wajen gyaran rijiyoyin burtsatse a yankin.

Yanzu-yanzu:Kotu ta baiwa hukumar zaben Kano umarni Kan zaben kananan hukumomi

Bidiyon – wanda ya karaɗe shafukan sada zumunta – ya janyo wa gwamnatin jihar suka daga mutanen ciki da wajen jihar Sokoto.

To sai dai cikin wani martani da gwamnatin jihar ta yi, ta fayyace yadda aka kashe kuɗin saɓanin yadda mutane suka fahimta.

Cikin wata sanarwa da kakakin gwamnan jihar, Abubakar Bawa, ya fitar ya ce ba gyaran burtsatsen gwamnan ke nufi ba, yana nufin gina sabbi.

Kotu ta tusa keyar alƙalin bogi zuwa gidan yari a Kano

Ya ƙara da cewa aikin na haɗin gwiwwa ne tsakanin gwamnatin jihar da wani shirin Bankin Duniya don samar da ruwan sha.

“Batun shi ne gwamnatin jiha tare da haɗin gwiwar Bankin Duniya ƙarƙashin shirin ACReSAL, sun tona sabbin rijiyoyin burtsatse masu amfani da hasken rana a garuruwan Munki da Marnona da Dinawa da Lugu da kuma Wurno, sai kuma gina katangar killace rijiyoyin da kuma aikin shingensu mai tsawon kilomita 40 a kan kuɗi naira biliyan 1.2”, kamar yadda sanarwar ta yi ƙarin haske.

Sanarwar ta ci gaba da cewa gwamnatin ta ɓullo da aikin ne domin magance matsalar ƙarancin ruwa da al’ummomin yankunan suka jima suna fuskanta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rasuwar Buhari: Majalisar Nigeria ta dakatar da duk aiyukanta

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Majalisar dokokin Nigeria ta dage zamanta...

Gwamnati ta baiwa ma’aikata hutu saboda rasuwar Muhammad Buhari

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gwamnatin jihar Katsina karkashin gwamna Umar...

Bayan tura Kashim ya taho da gawar Buhari, Tinubu ya ba da umarnin sassauta Tutar Nigeria

Shugaban kasa Bola Tinubu ya bada umarnin ayi kasa...

Yanzu:yanzu: Tsohon shugaban Nigeria Buhari ya rasu

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un!!! Allah yayi wa tsohon shugaban...