Farashin Man Fetur ya yi tashin gwauron zabi a Nigeriya

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Rahotanni na tabbatar da cewa kamfanin mai na kasa NNPC ya kara farashin litar man fetur a duk fadin Nigeria.

Kamfanin na NNPC dai a jiya litinin ya koma da cewa yana fama da matsalar Kuɗi, Kuma kawai sai yau (Talata) aka wayi gari da maganar karin farashin kudin wanda ya kai Naira 904 a jihar kano.

A jihar Lagos kuma a safiyar wannan rana ana sayar da man ne akan kudi Naira 855 maimakon Naira 568.

Haka a birnin fatakwal na jihar Rives yanzu na sayar da man fetur din akan kudi Naira 925.

PDP ta tsayar da ranakun zabukan shugabanninta

Duk da dai har yanzu a hukumance kamfanin na NNPC bai fito ya bayyana Karin kudin Man ba, amma ana ganin Karin yana da nasaba ya yadda man yake isowa Nigeria daga Inda aka sayo shi, saboda kuɗin dako da wasu hidindimu.

Yanzu haka farashin litar man fetur ya yi tashin gwauron zabo zuwa Naira 1,200 a gidajen mai a Jihar Kano.

Gidajen mai masu zaman kansu sun kara farashin ne a safiyar Talata.

Sun dauki matakin ne a daidai lokacin da gidajen man. NNPCL suka ƙara nasu farashin zuwa N904 a jihar.

Talla
Talla

A halin da ake ciki dai masu ababen hawa sun yi dogayen layi a gidajen man NNPCL da ke Kano domin shan mai.

Wani jami’i a wani gidan man NNPCL da ke Kano ya shida wa daily trust cewa suna jiran a ba su umarnin sayar da man a akan sabon farashi.

“Kawai zuwa muka yi aiki muka ga an canza farashi kamar yadda kake gani. Yanzu umarni kawai muke jira.

Wani wanda ya je shan mai ya ce, “mun shiga uku a ƙasar nan, ima muka dosa? Wannan babban abin takaici ne.

Mahaifiyar tsohon shugaban Nigeria ta rasu

Shi kuma Ibrahim Saleh ya bayyana yadda ba ya ba a matsalar mai amma yanzu fetur na kamshin turaren dan goma a Najeriya..

“Na tuna lokacin da aka taba rage farashin lurar fetur a lokacin mulkin Yar’Adua zuwa N65, na zan taba manta wannan abu ba.

“Amma yanzu duk farashin abin da aka kara a ƙasar nan ba ya raguwa.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Ba za mu lamunci cin zarafi ko tozarta wasu da sunan Tashe ba – Hukumar Hisbah

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Hukumar Hisba ya jihar kano ta...

Da dumi-dumi: El-Rufa’i ya fice daga jam’iyyar APC

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i ya tabbatar da...

2027: Atiku Abubakar ya bayyana matsayarsa game da kasancewarsa a PDP

  Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya musanta rahotannin...

Cikakken Bayani Kan Yan Bindigar da Yansanda Su Ka Kama a Kano

Daga Rahama Umar Kwaru   Rundunar yansanda ta kasa reshen jihar...